Bincike: Yadda Manyan Najeriya da Iyalansu 61 Suka Saye kadarorin $270m a Amurka
- Bincike ya gano kadarori 284 da kimarsu ta kai $271m mallakin jami’an Najeriya 61 da iyalansu a Amurka
- Mafi yawa daga cikin kadarorin an mallake su ne a daidai lokacin da jami’an ke kan rike da mukaman gwamnati
- Kusan 20% na kadarorin an saye su ne da tsantsan tsabar kudi, ragowar kuma da alamar tambaya game da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
America - Wani sabon bincike ya gano cewa ‘yan Najeriya 61 suna da alaka da wasu kadarori sama da 280 a kasar Amurka.
Tsofaffin jami’ai da masu-ci a yau, iyalansu, abokan huldarsu da wasu kamfanoninsu aka samu sun mallaki kayan $271m.

Source: Getty Images
'Yan Najeriya sun saye kadarorin $270m a Amurka
Rahoton Premium Times ya ce an mallaki wadannan kaya ne daga 1991 zuwa yanzu, daga ciki an saye 152 a lokacin ana ofis.
An gabatar da bayanan binciken da aka yi ranar Talata a Abuja, aka nuna kazamar dukiyar da ‘yan Najeriya suka tara a Amurka.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Platform to Protect Whistleblowers in Africa (PPLAAF) da hadin guiwar Anti-Corruption Data Collective (ACDC) suka yi aikin nan.
‘Yan siyasa da masu kudin kasar nan sun shiga harkar sayen gidaje a Amurka, binciken ya kuma nuna hadarin wannan kasuwanci.
Wasu jami’an gwamnati suna kan mukamansu suka yi amfani da kamfanoni ko suka fake da wasu wajen sayen kadarori a waje.
Ana mallakar kadarori da kudi marasa tushe
Cibiyar PPLAAF ta ce ba a san ta yadda aka fanshi 81% na kadarorin ba, wanda ana maganar farashinsu a yau ya haura $230m.
Wasu kadarori 147 kuwa, jami’an sun same su ne a hanyar fakewa da sunayen iyalansu. A nan ma ana zancen an kashe har $111m.
Akwai kadarori 104 na kimanin $140m da aka saye su ta wasu kamfanoni kamar yadda aka gano.
Masu dukiyoyin suna cikin mutanen da ake bincike
Abin ban tsoron shi ne, 39 cikin mutane 61 da suke da wannan arziki, suna cikin wadanda ake zargi da rashin gaskiya a Najeriya.
Daga ciki akwai Sambo Dasuki, Abdulrasheed Maina, Sanata Orji Uzor Kalu, Chimaroke Nnamani da irinsu Ronald (Roland) Ewubare.
Akwai Stella Oduah, Dibu Ojerinde, marigayi Alex Badeh, Abdulrahman Dambazau, Dr. Chris Ngige, Willie Obiano da marigayi Ajibola Ajimobi.
Irin wadannan mutane suna da alaka kadarori da 195 da darajarsu ta kai $208m a kasuwa.
PLAAF tana so a karbo kudin sata daga Amurka
Sakamakon wannan bincike, shugaban PPLAAF, Jimmy Kande, ya ce an fahimci yadda kudin talakawa suke karewa a kasar waje.
Kande ya bukaci a yi bincike da kyau domin a karbo wadannan dukiyoyi, a dawo da su cikin baitul-mali domin amfanin talakan kasar.
‘Yan siyasa da suka rike mukamai, ‘yan majalisa, shugabanni da jami’an tsaro da sauran manyan gwamnati ne gaba a tara dukiyar.

Source: Getty Images
Kudi da aka gano a dakin dalibin Najeriya a Turai
Kwanaki aka ji labarin wani bidiyoyo da ya nuna yadda hukumomi a kasar Birtaniya suka shiga gidan wani dalibi dan Najeriya.
Jami'an tsaron kasar wajen sun gano tsabar kudi da suka kai $8.5m da aka boye a cikin wani akwati a gidan dalibin makaranta.
Ana zargin cewa makudan kudin na da alaka da harkallar haramun kamar ta'addanci, damfara ko kuma cinakayya ta kwayoyi.
Asali: Legit.ng
