Naja da Sauran Mata 10 da Suka Samu Shiga Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku

Naja da Sauran Mata 10 da Suka Samu Shiga Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku

Abuja - ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya fitar da kwamitin da zai yi masa kamfe a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

‘Yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar ba su da yawa. Atiku ya ce an duba halin da kasa ta ke ciki ne a yau.

Kamar yadda Phrank Shaibu ya sanar a X da sauran kafofin sadarwa na zamani, Ibrahim-Imam ne jagoran kamfe na kasa.

Legit hausa ta duba jerin, ta tattaro matan da suke cikin kwamitin yakin zaben.

Matan ADC da ke kwamitin tallata Atiku Abubakar

Jerin ya kunshi tulin maza amma babu matasa da mata wadanda sun kunshi kaso mai yawo na al’umma a Najeriya a yanzu.

1. Ireti Kingibe

Sunan Ireti Kingibe ya fito a cikin ‘yan majalisar da za su rika ba kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar ADC shawara.

Kara karanta wannan

Matashin da aka sa a kwamitin yakin zaben Obi da Kwankwaso ya cire kan shi

Sanatar mai wakiltar Abuja kwararriyar ‘yar siyasa ce, ita kadai ce mace da ta ke rike da tutar jam’iyyar ADC a majalisar dattawa.

2. Naja’atu Mohammed

Ita ma Hajiya Naja’atu Mohammed tana cikin mashawartan kwamtin yakin zaben na ADC, akwai sunanta cikin mutane biyar na kwamitin.

‘Yar siyasar za ta yi aiki a karkashin jagorancin John Oyegun da Lawal Batagarawa wanda aikin jam’iyya ya rika hada ta da shi a baya.

3. Patricia Akwashiki

Patricia Akwashiki ta fito a cikin manyan mashawartan kamfen shugaban kasa a jam’iyyar ADC, tana cikin mata kalilan a kwamitin takarar.

Sanata Akwashiki ta taba wakiltar Nasarawa ta Arewa kuma dattijuwar ta shafe shekara da shekaru tana Ministan wayar da kan jama’a.

4. Nana Kazaure

Kwamitin yana dauke da sunan Nana Kazaure a cikin jagororin harkokin yada labarai da sanarwa, ita ce kakakin kamfe a babban zabe.

A zaben 2023, Nana ta rike wannan mukami, ta kasance kakakin kwamitin tallar Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed a jam’iyyar LP.

5. Naomi Labari

Naomi Labari na cikin manyan wadanda ke da alhakin tallar Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi, za ta yi aiki a karkashin Dino Melaye.

Kara karanta wannan

Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta

Shugabar matan ta jam’iyyar ADC tana cikin kwamitin harkar tattaro jama’a a yakin zaben badi.

6. Rhoda Sanda

Madam Rhoda Sanda ce Alhaji Atiku Abubakar ya bari da dawainiya da kungiyoyi masu zaman kansu a zaben shugaban kasa na 2027.

Sanda wanda tana cikin jagororin mata a tafiya Obidient ta cigaba da zama a ADC bayan tsohon mai gidanta a siyasa, Peter Obi ya koma NDC.

7. Zainab Buba Galadima

A kwamitin da ke kula da kungiyoyin magoya baya, an hada Zainab Buba Galadima da aiki kan harkokin jinsi domin ganin nasarar ADC.

Zainab Buba Galadima ta dade a harkar siyasa kuma ta yi gado. Ta taba aiki da Yemi Osinbajo kuma ta rike shugabanci a birnin Abuja a APC.

8. Lauretta Onochie

Wata tsohuwar hadima a fadar shugaban kasa da ta samu shiga kwamitin yakin zaben Atiku/Amaechi ita ce madam Lauretta Onochie.

Onochie ta kasance cikin mataimakan Muhammadu Buhari kafin ya ba ta mukami a hukumar NDDC, za ta kula da harkokin na’urori yayin kamfe.

Kara karanta wannan

Baraka ta hargitsa jam'iyyar NDC da tafiyar Obi da Kwankwaso daga fara kamfen

Wasu mata da suke cikin kwamitin yakin neman zaben sun hada da:

9. Moji Rhodes Vivour

10. Dr. Amina Mohammed

Atiku ya ba Nasir El-Rufai aikin kamfe

An ji labari kasancewar Nasir El-Rufai a matsayin mataimakin shugaba ya jawo abin magana ganin yana tsare a hannun hukuma.

Tsohon gwamnan na Kaduna mataimakin shugaban kwamiti ne a yakin neman zaben Atiku Abubakar/Rotimi Amaechi.

Babban 'dan adawar zai taya Ibrahim-Imam aikin kamfe kamar yadda Phrank Shaibu ya fitar da sanarwa a yammacin Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng