An Ajiye Atiku, Kwankwaso: An Fadi Mutum 1 da Zai Iya Kwace Mulki a Hannun Tinubu

An Ajiye Atiku, Kwankwaso: An Fadi Mutum 1 da Zai Iya Kwace Mulki a Hannun Tinubu

  • Nana Kazaure, tsohuwar kakakin yakin neman zaben Obit-Datti a 2023 ta yi hasashen wanda zai iya lashe zaben 2027 mai zuwa
  • 'Yar gwagwarmayar, ta ce Peter Obi zai iya lallasa Shugaba Bola Tinubu a zaben mai zuwa idan majalisa ta amince da wata doka
  • Kazaure ta ce Obi na da damar cin zabe a 2027 idan majalisa ta amince da dokar ba 'yan takara damar tsayawa zab ba da jam'iyya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohuwar kakakin yaƙin neman zaɓen Obi-Datti a zaben 2023, Nana Sani Kazaure, ta ce Peter Obi na iya kayar da Shugfaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Nana Sani Kazaure ta bayyana cewa matasa suna kara mara wa Obi baya, musamman saboda rashin jin daɗin mulkin Tinubu a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Ana zancen kudirin haraji, an sa rana da lokutan shirya zanga zanga

Nana Kazaure ta yi magana kan yiwuwar nasarar Peter Obi a 2027
Nana Kazaure ta yi bayanin yadda Peter Obi zai iya lashe zaben 2027. Hoto: @PeterObi, @officialABAT
Asali: Facebook

"Peter Obi zai iya cin zaben 2027" - Kazaure

A zantawarta da jaridar Punch, Kazaure ta ce Obi ya samu ƙarin farin jini cikin shekara guda saboda rashin nasarar ayyukan gwamnati mai ci a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Obi shine wanda matasa ke so, saboda sun fi jin zafin wannan gwamnatin fiye da ta baya," a cewar Nana Kazaure.

Dangane da matsalolin cikin gida a jam’iyyar Labour, ta ce Obi na iya amfani da dokar zaɓen 'yan takara masu zaman kansu idan majalisa ta tabbatar da ita kafin zaben 2027.

Nana Kazaure ta magantu kan takarar Obi

Ta yi tsokaci kan tattaunawar majalisar tarayya kan dokar da zata ba da dama ga mutum ya tsayawa takara ba tare da shiga wata jam'iyya ba.

"Tsohon gwamnan jihar na Anambra na iya amfani da tsarin takara ba tare da jam'iyya ba idan har kudurin ya samu amincewar majalisa kafin zabe na gaba.

Kara karanta wannan

Kwamitin APC ya fara zaman sulhu, an dauko hanyar sasanta 'yan jam'iyya

"Idan har wannan dokar ta tabbata a Najeriya, to ina da tabbacin Peter Obi zai iya lashe zabe. Majalisar tarayya na ta magana kan yin takara ba tare da jam'iyya ba."

- A cewar Nana Kazaure.

LP ta fara shirin kawar da Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar LP ta fara shirye-shiryen kawar da Shugaba Bola Tinubu daga kan mulki a zaben 2027 mai zuwa.

Domin gujewa kalubalen da ta fuskanta a zaben 2023, jam'iyyar LP ta fara gina tsarin jagoranci a jihohi 36 domin tunkarar zaɓen 2027 cikin ƙarfi da tsari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.