Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Baiwa Hadimarsa Babban Mukami a Gwamnatinsa

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Baiwa Hadimarsa Babban Mukami a Gwamnatinsa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Lauretta Onochie a matsayin shugabar hukumar NDDC
  • Shugaban kasar ya mika sunanta tare da wasu mambobin hukumar su 15 zauren majalisa a yau Laraba don tantance su
  • Idan za ku tuna, Buhari ya taba nada hadimar tasa a matsayin kwashinar zabe ta jihar Delta amma lamarin bai tabbata ba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mai bashi shawara kan kafofin sadarwar zamani, Lauretta Onochie, a matsayin shugaban hukumar ci gaban yankin Neja Delta (NDDC).

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kasar ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

A cikin wasikar, Buhari ya kuma sanar da zabar wasu mutane 15 a matsayin mambonin kwamitin NDDC, Thisday ta rahoto.

Buhari
Da Dumi-dumi: Buhari Ya Nada Lauretta Onochie a Matsayin Shugabar Hukumar NDDC Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Wasikar, wacce aka karanta a zauren majalisar a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, ya bukaci majalisar dattawan da ta tabbatar da mutanen da aka zaba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Kowa A Jiha Ta Masoyin Buhari Ne": Gwamnan PDP Ya Aika Saƙo Mai Kaɗa Hanta Ga Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya taba nada Onochie kwamishinar zabe amma majalisa ta ki tabbatar da ita

A baya Buhari ya zabi Onochie a matsayin kwamishinar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta domin wakiltan jihar Delta.

Sai dai kuma, zaban nata ya haddasa takkadama mai zafi, inda yan siyasa da dama da kungiyoyin jama’a suka nemi aki tabbatar da ita kan hujjar cewa ita din ita daukar bangare a siyasa don haka bata cancanci aiki a wuri irin INEC ba.

A kan haka, har babbar jam'iyyar adawar kasar wato PDP ta gudanar da zanga-zanga a harabar majalisar don nuna adawarta ga nadin hadimar shugaban kasar.

An kuma yi zargin cewa tana dauke da katin shaidar kasancewarta yar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), amma sai ta karyata hakan sau uku a yayin tantance ta.

Kara karanta wannan

Gara in Mutu da dai in Gazawa Magoya Bayana, Peter Obi

Sai dai kuma, daga karshe majalisar dattawan ta ki amincewa da nadin nata.

Shugaban kwamitin tantancewar a lokacin, Sanata Kabiru Gaya ya ce akwai kwamishinan INEC daga jihar Delta a kan kujera inda daga nan ne Onochie ta fito, kuma tabbatar da nadinta zai saba tanadin kundin tsarin mulki.

A wani labarin, ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola, ya ce yan Najeriya za su dunga tunawa da Buhari saboda yadda ya rusa kungiyar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel