Duk da Yana Tsare, Atiku Ya Nada Malam Nasir El Rufai a Kwamitin Yakin Neman Zaben ADC
- Atiku Abubakar ya naɗa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓensa
- An bayyana kwamitin a matsayin tsari mai sauƙi da aka gina kan ƙwarewa, riƙon amana da haɗin kan ƙasa
- Kashim Ibrahim-Imam ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Sanata Austin Akobundu zai kasance Darakta-Janar naYaƙin Neman Zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya naɗa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na jam’iyyar ADC.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

Source: Facebook
Daiky Trust ta ruwaito cewa rahotannin da aka wallafa a ranar Alhamis sun tabbatar da cewa El-Rufai zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.

Kara karanta wannan
Kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya ta yi magana kan kama Atiku gabanin zaben 2027
El-Rufai na tsare a hannun ICPC
El-Rufai na hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaƙa (ICPC), yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume da gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna suka shigar.
Hukumar ICPC ta tabbatar a baya cewa yana hannunta bisa umarnin kotu yayin da ake ci gaba da shari’ar. An kama Malam Nasir tun watan Fabrairu kuma har yanzu yana tsare.
Atiku ya nada kwamitin kamfen ADC
Phrank Shaibu, kakakin Atiku kuma Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na yaƙin neman zaɓen, ya ce Atiku ya amince da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe.
Sanarwar ta ce:
“Mai Girma Atiku Abubakar, GCON, ya amince da kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe da kuma Kwamitin Gudanar da Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa mai wanda aka tsara bisa dabaru.
“Girma da tsarin kwamitin sun yi daidai da halin da ƙasa ke ciki da kuma tsananin matsin tattalin arzikin da miliyoyin ’yan Najeriya ke fuskanta.
"A lokacin da ake tilasta wa iyalai su gudanar da rayuwa da ƙarancin abin da suke da shi, yaƙin neman zaɓen ma dole ne ya nuna irin wannan ladabi, taka-tsantsan da fahimtar halin da jama’a suke ciki.
Mukamin da Atiku ya ba Nasir El-Rufai
Sanarwar ta ce Kashim Ibrahim-Imam ne zai zama shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe ADC, inda aka bayyana shi a matsayin gogaggen mai dabarun siyasa da gudanarwa.
El-Rufai, tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya kuma tsohon Gwamnan Kaduna, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.

Source: Facebook
A cewar sanarwar, El-Rufai zai kawo gogewarsa a harkokin gudanarwa, tsara harkokin siyasa da jagorancin zartarwa wajen tafiyar da kwamitin.
Nauyin da aka ɗora masa ya haɗa da daidaita manyan harkokin siyasa da kuma hulɗa da muhimman masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar.
Wasu gwamnoni na shirin hadewa da Atiku
Kun ji cewa ana rade radin wasu gwamnonin APC da ba su gamsu da wasu tsare-tsaren jam’iyyar ba sun fara duba yiwuwar kulla alaƙa da Atiku Abubakar gabanin zaben 2027.
Rahotanni sun ce matakin na da nasaba da damuwar da wasu gwamnonin ke nunawa kan tasirin ƙungiyar Rainbow Coalition da ke ƙarƙashin Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng
