Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta
- Atiku Abubakar zai biya kudin karatun bokon Yusuf Aliyu da yake harkar aikin hakar ma’adanai a jihar Neja
- Yaron ya bada labarin abin da ya faru da su lokacin da jami’an hukumar NSCDC suka rutsa abokan aikinsa
- Atiku ya yi kira da a kare yaron saboda gudun a kai masa hari a dalilin bayanan da ya bankado a hirar da aka yi da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - Atiku Abubakar ya ji tausayin daya daga cikin kananan yaran da aka gani wajen hakar ma’adanai a jihar Neja.
Bidiyon Yusuf Aliyu ya rika yawo a kafafen sada zumunta bayan mutuwar wasu abokan aikinsu 37 da NSCDC ta kama.
Atiku Abubakar ya ga bidiyon Yusuf Aliyu
A shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya ce zuciyarsa ta yi rauni da ya ga bidiyon hirar wannan karamin yaro.
Atiku Abubakar ya ce ya shirya daukar dawainiyar karatun wannan yaro da ya ce da baiwarsa, kyau a ce yana karatu cikin aji.
‘Dan siyasar ya yaba da basira da karfin halinsa, yake ganin bai dace da hakar ma’adanai ba.
"Na kalli bidiyon Yusuf Aliyu sau da dama, kuma ko yaushe zuciya tana rauni.
Yaro mai basira, karfin iya bayani da karfin hali irin wannan kyau ya kasance a aji yana gina gobensa - ba ya yi ta fama cikin al’ummar da ke zagaye da zinari a birne amma suna cikin talauci ba.
Ba zan kalle shi in ga mai hakar ma’adanai a kan ka’ida ba. Ina ganin yaron Najeriya da kasarsa ta gaza, maimakon ta kare shi.
Na ga basira kudundune cikin talauci da tulin alkawarin da shugabannin suka gagara cikawa.
- Atiku Abubakar
Atiku ya nemi al'umma ta kare yaron
‘Dan takaran shugaban kasar na ADC ya kuma yi kira da a ba yaron kariya, ya bukaci jama’a su guji fallasa shi ko kuma iyalinsa.
Alhaji Atiku yana tsoron cewa za a iya kai masa ko danginsa hari a jihar Neja saboda bayanan da ya fallasa.
A zantawar da aka yi da yaron, ya tabbatar wa duniya da cewa ba hakar ma’adanai suke yi ba bisa ka’ida ba kamar yadda ake zargi.
Yusuf ya bada labarin yadda jami’an NSCDC suka auko masu, suka rika harbin jama’a duk da cewa ba su saba wata dokar kasa ba.
Atiku Abubakar zai kai shi makaranta, ya ce:
"A shirye nake na bada gudumuwa wajen karatunsa kuma in tabbatar da cewa talauci ba ta lullube basirarsa da muka gani."
- Atiku Abubakar
A jawabinsa, ya soki yadda gwamnatin Tinubu ta sha bam-bam da ta Muhammadu Buhari da ya kirkiro shirin PAGMI lokacin yana mulki.
‘Dan adawan ya zargi gwamnati da kama talakawa tana garkame su haka kurum da sunan suna hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Atiku ya zargi Tinubu da dabara da tallafin mai
Wani hadimin ‘dan takaran shugaban kasa a ADC ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta maido tallafin fetur amma a cire daga an yi zabe.
Hadiminsa ya bayyana cewa wannan dabara ce ta siyasa, domin ana shirin sake cire tallafin kai tsaye da zarar an kammala zaben 2027.
Atiku Abubakar ya jaddada cewa zai fito da tsarin tallafi na gaskiya wanda zai rage kudin tace fetur a gida maimakon yaudarar jama'a.
Asali: Legit.ng

