Matashin da Aka Sa a Kwamitin Yakin Zaben Obi da Kwankwaso Ya Cire Kan Shi

Matashin da Aka Sa a Kwamitin Yakin Zaben Obi da Kwankwaso Ya Cire Kan Shi

  • sFitar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da OK ta yi, ya jawo mata matsala da NDC da 'ya 'yanta
  • Mallam Jabir Ibrahim Yaro ya ce kungiyar ba ta tuntube shi ba, ta yi gaban kan ta wajen sa shi a kwamitin
  • Matashin ‘dan siyasar kuma masoyin Peter Obi ya bukaci a cire sunan shi sannan a fito a nemi afuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Jabir Ibrahim Yaro ya yi watsi da jefa sunan shi da aka yi cikin jerin kwamitin yakin zaben Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Kungiyar OK mai goyon bayan Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ta yi azarbabin fitar da wadanda su yi mata aikin kamfe a zaben 2027.

Peter Obi da Kwankwaso
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso wajen kamfe a Kaduna da takardar sanarwar Mallam Jabir Ibrahim Yaro Hoto: SaifullahiHon/Mallam_jabeer
Source: Twitter

Jabir Ibrahim Yaro bai cikin kwamitin kamfen OK

Mallam Jabir Ibrahim Yaro ya yi maza ya fito shafinsa na X ya yi karin haske ganin sunansa yana cikin wadanda aka sa a kwamitin.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya jero gwamnonin jam'iyyar APC 3 da suka huro masa wutar adawa

Matashin ‘dan siyasar ya nuna bai san an yi wannan ba, kuma bai ba kungiyar OK umarnin cusa shi cikin ‘yan kwamitin kamfe ba.

Mallam Jabir Ibrahim Yaro wanda ya fi shahara da Mallam Jabir ya yi watsi da wannan lamari tare da neman afuwa daga kungiyar siyasar.

Sanarwar ta bukaci Mr. John Ugulu ya yi gaggawar cire sunan shi, kuma ya bada hakuri na amfani da sunan ba tare da samun izininsa ba.

Mallam Jabir ya rabu da Peter Obi?

Sai dai wannan sanarwa ba ta nufin Mallam Jabir ya yi watsi da gwaninsa, Peter Obi.

Har gobe yana tare da Obi da takararsa kuma yana jiran a fitar da jerin ‘yan kwamitin yakin zaben shugaban kasa na ainihi a hukumance.

'Dan siyasar yana cikin 'yan ga-ni-kashe-nin Obi kuma har ya nemi ya fito neman tikitin takarar gwamnan Kaduna a jam'iyyar NDC a 2027.

Kara karanta wannan

Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta

Sanarwar da ya fitar a shafinsa

Ga abin da ya rubuta:

SANARWA
"Ni, Mallam Jabir Ibrahim Yaro, ina bayyana wa karara cewa ba ni da wata alaka da jerin sunayen mutane 59 da aka sanar a matsayin Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban kasa, wanda Mista John Ugulu ya bayyana a karkashin OK Movement.
Ba a tuntube ni ba, ba a nemi ra’ayina ba, kuma ba a sanar da ni game da wannan kwamiti ba. Haka kuma, ban taɓa amincewa a saka suna na cikin kwamitin ba.

‘Dan siyasar kuma manomi ya shaida wa duniya cewa babu abin da ya hada shi da tafiyar Ok da Mista John Ugulu suke jagoranta.

Legit Hausa ta lura wannan kungiya ta OK tana bambanci da Obidents da aka sani da goyon bayan Obi.

Mallam Jabir ya cigaba da cewa:

"Saboda haka, ina watsi da duk wata sanarwa ko wakilci da zai nuna cewa ni mamba ne ko kuma ina da wata alaka da wannan kwamitin da aka ambata.

Kara karanta wannan

El Rufai: Limami ya aika wa Uba Sani sako a mimbarin Juma’a, ya fadi abin da Tinubu ya fada

Har yanzu ina nan kan goyon bayana ga Jagoranmu, Mai Girma Peter Obi, kuma ina jiran sanarwar hukuma game da kwamitin yaƙin neman zaɓensa daga hukumomin da abin ya shafa.
Ina buƙatar Mista John Ugulu ya gaggauta cire sunana daga cikin jerin, tare da neman afuwar amfani da suna na ba tare da sanina ko amincewata ba."
Sa hannu:
Mallam Jabir Ibrahim Yaro
22 ga Satumba, 2026

Ana rigima maimakon kamfe a NDC

Labari ya zo dangane da yadda kungiyar OK da shugabannin NDC suka bude yakin zabe da rikici maimakon a dage wajen tallata 'yan takararsu a 2027.

Kafin jam'iyyar NDC ta fitar da 'yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, OK ta fitar da wadanda za su tallata Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Atiku Abubakar ya yi nisa wajen kamfe a inuwar ADC haka zalika kwamitin yakin zaben APC a karkashin jagorancin Abdulaziz Yari ya kama aiki tun tuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng