Jami’ai 3 daga Gwamnatin Buhari da ke cikin Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027
Abuja - Hukumar INEC ta fitar da sunayen mutanen da za su yi takarar shugaban kasa a babban zabe da yake tafe a badi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
‘Yan takaran 18 za su dage wajen ganin sun raba Bola Ahmed Tinubu da kashim Shettima da fadar Aso Rock Villa a 2027.
Sakatariyar hukumar INEC, Rose Oriaran-Anthony ta fitar da sunayen ‘yan takara 18 da abokan gaminsu da jam’iyyarsu.

Source: Facebook
Bayani kan masu takarar shugaban kasar 2027
A cikinsu akwai maza 16 da kuma mata biyu, sai dai a cikinsu an fi sanin wadanda suka tsaya a APC, ADC, NDC da APM.
Matan su ne Ada Elizabeth Fredrick Okwori na NDP sai kuma Nkem Esther Okerekeda aka tsaida a karkashin NRM mai adawa.
Patience Ndidi Key da Nafisat Usaku Abubakar kuwa sun fito neman mataimakan shugaban kasa a jam’iyyun DLA da YPP.
Mutane 36 masu takara a zaben shugaban kasa
Wadanda INEC ta san da takararsu zuwa yanzu ne:
1. APC: Bola Tinubu (74) / Kashim Shettima (59)
2. ADC: Atiku Abubakar (79) / Chibuike Rotimi Amaechi (61)
3. NDC: Peter Gregory Obi (65) / Musa Mohammed Rabiu Kwankwaso (69)
4. LP: Sunday Chibuzo Okereke (43) / Hajja Bintu Konto (54)
5. PDP: Sandy Ojang Onor (60) / Umaru Babangida (61)
6. AA: Rufai Adekunle Omo-Aje / Shehu Hussaini
7. ADP: Aliyu Abbas-Bin / Chinazam Ike
8. APP: Kabiru Yusuf / Peace Egobia Ofordile
9. AAC: Omoyele Sowore / Haruna Garba Magashi
10. APM: Oluseyi Abiodun Makinde (58) / Musa Lawal Daura
11. BP: Sunday Adenuga / Usman Turaki Mustapha
12. DLA: Moses Olusoji Adebisi / Nafisat Usaku Abubakar
13. NDP: Ada Elizabeth Fredrick Okwori / Uchenna Anthony Chukwuemeka
14. NRM: Nkem Esther Okereke / Nasir Muhammed Sulaiman
15. PRP: Donald Duke / Kabiru Rabiu
16. SDP: Adewole Ebenezer Adebayo / Usman Muhammed Bugaje
17. YPP: Peter Ada Agada / Patience Ndidi Key
18. ZLP: Daniel Daberechukwu Nwanyanwu / Hassan Khalid
Mutanen Buhari da suke takara a 2027 ba
Legit Hausa ta tattaro wasu cikin wadanda suka yi aiki da marigayi Muhammadu Buhari da za su kara da Bola Tinubu.
1. Rotimi Chibuike Amaechi
Rotimi C. Amaechi yana cikin wadanda aka dama da su a gwamnatin Muhammadu Buhari, yanzu shi ne abokin gamin Alhaji Atiku Abubakar.
Kafin zamansa ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a ADC, ya yi Ministan sufuri a gwamnatin APC kuma shugaban kamfe sau biyu.
Amaechi ya nemi APC ta tsaida shi a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa, Bola Tinubu ya doke shi kuma ya yi nasara a babban zabe.
2. Lawal Musa Daura
Lawal Musa Daura mai shekara 73 a duniya ya rike shugabancin hukumar DSS watanni uku bayan Buhari ya hau mulki har zuwa 2018.
Babban jami’in ya rasa matsayinsa na lokacin da Yemi Osinbajo ya zama shugaban kasa na rikon kwarya da shugaban kasa yake jinya.
Daura ya shigo siyasa kuma ya zabi jam’iyyar ADC domin takarar gwamna. Yau shi yake yi wa APM takarar mataimakin shugaban kasa.
3. Chukwuemeka Nwajiuba
Hon. Chukwuemeka Nwajiuba yana sa ran shi ne ‘dan takaran jam’iyyar LPP a zaben shugaban kasa na 2027 a Najeriya.
‘Dan siyasar bai cikin wadanda INEC ta wallafa sunansu, amma daga baya jam'iyyar LPP tana mika masa tuta a birnin Abuja.
Chukwuemeka Nwajiuba tsohon ‘dan majalisar tarayya ne kuma ya zama karamin ministan ilmin a mulkin Buhari a 2019.
Sauran ‘yan takara masu alaka da Buhari
Akwai Usman Bugaje wanda shugaba Buhari ya zabe shi ya zama minista a gwamnatinsa, amma ‘dan siyasar ya ki karbar tayin.
Dr. Bugaje wanda tsohon ‘dan majalisar tarayya ne shi ne yake takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta SDP a 2027.

Source: Getty Images
Rabiu Kwankwaso ya kasance a jam’iyya guda da tsohon shugaban kasar, amma bai taba ba shi wani mukami a gwamnatinsa ba.
A 2018 Kwankwaso ya bar jam’iyyar APC zuwa PDP da nufin zama shugaban kasa. A zaben badi shi ne abokin gamin Peter Obi na NDC.
Manyan 'yan takaran sanatoci a zaben 2027
Wannan dogon rahoto ya dauko sunayen duka ‘yan takara da ke neman zama sanatocin duka mazabu 109 a manyan jam’iyyun siyasa.
An ga manyan ‘yan takara da Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da cikakken jerin masu neman kujerun Majalisar Dattawa.
APC ta fi kowace jam'iyya 'yan takara inda su kuwa 'yan adawa suke da wasu mazabun da ba su iya tsaida mai neman zama sanata a majalisa ba.
Asali: Legit.ng



