Dangote Ya Fara Sayar da Hannun Jarin Matatarsa da Kafar Dama, Ya Samu Sabon Matsayi a Duniya

Dangote Ya Fara Sayar da Hannun Jarin Matatarsa da Kafar Dama, Ya Samu Sabon Matsayi a Duniya

  • Arzikin Aliko Dangote ya tashi daga dala biliyan $31.4 zuwa $51.3, lamarin da ya ƙara masa dala biliyan $19.9 cikin kwana guda
  • Bayan ƙarin arzikin, matsayin Dangote a jerin attajiran duniya na Forbes ya tashi daga na 76 zuwa na 36
  • Ƙarin darajar Dangote ya zo ne yayin da matatar Dangote ta fara sayar da hannayen jarinta ga jama'a ta hanyar IPO a kasuwar NGX

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Aliko Dangote, wanda ya kafa Dangote Group kuma shugaban matatar Dangote, ya zama attajirin da ke da arzikin dala biliyan $51.3.

A cewar jerin attajiran duniya na Forbes Real Time Billionaires, arzikin Dangote ya ƙaru da kashi 63.37 cikin 100, daga dala biliyan $31.4 da aka kiyasta yana da su ranar Lahadi zuwa $51.3bn ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai kazamin harin da ya jawo asarar rayuka da kona gidaje

Arzikin Dangote ya karu
Hamshakin attajiri, Aliko Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan ya nuna cewa arzikin ɗan kasuwar ya ƙaru da dala biliyan $19.9 cikin kwana guda, cewar rahoton The Cable.

Dangote ya haura matsayi 40 a jerin attajiran duniya

Bayan wannan gagarumin ƙarin arziki, matsayinsa a jerin attajiran duniya ya tashi daga na 76 zuwa na 36.

Ƙarin arzikin nasa ya zo ne a daidai lokacin da aka fara sayar da hannayen jarin matatar Dangote ga jama'a ta hanyar Initial Public Offering (IPO).

An kiyasta darajar kamfanin a dala biliyan 50, wato sama da Naira tiriliyan 60, bisa farashin musayar kuɗi na ranar 4 ga Satumban 2026.

Matatar Dangote ta fara IPO a NGX

Matatar Dangote ta fara IPO a ranar Litinin ta hannun kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX), inda take shirin tara Naira tiriliyan 2.15.

Kamfanin na son amfani da kuɗin wajen tallafa wa shirin faɗaɗa ayyukansa da darajarsa ta kai dala biliyan 40.

Kara karanta wannan

"Ba na son a kara kira na wanda ya fi kowa kudi a Afrika"; Dangote ya fadi sunan da yake so

Daga cikin shirye-shiryen akwai ƙara yawan man da matatar ke sarrafawa daga ganga 650,000 a kowace rana zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana.

Dangote ya yi hasashen $350bn

Da yake jawabi a shirin kamfanin mai taken ‘Fact Behind The List’, Dangote ya ce yana sa ran darajar matatar za ta kai aƙalla dala biliyan 350 nan da shekarar 2030.

A yayin IPO ɗin, wanda za a rufe a ranar 13 ga Oktoba, masu zuba jari za su samu damar sayen sama da hannayen jari biliyan 4.1 na matatar.

An saka farashin kowane hannun jari a N525, yayin da mafi ƙarancin adadin da mutum zai iya saya shi ne hannaye 10, wanda ya kai N5,250.

Daga ina arzikin Dangote yake?

Arzikin Dangote na dala biliyan 51.3 ya samo asali ne daga jarinsa a masana'antu daban-daban.

Ya mallaki manyan jarin kasuwanci a fannonin siminti, sukari, banki, mai da iskar gas, baya ga sauran harkokin kasuwancin Dangote Group.

Arzikin Dangote ya karu
Aliko Dangote na gabatar a wajen taro Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Dangote ya rada wa kansa sabon suna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban rukunin kamfonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce ba ya son a ƙara kiransa mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka.

Dangote ya bayyana cewa ya fi son a san shi a matsayin attajirin da ke taimakawa wajen samar da arziki ga wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng