Siyasar Kaduna Ta Dauki Zafi, Makusantan El Rufai Sun Koma wajen Uba Sani a APC

Siyasar Kaduna Ta Dauki Zafi, Makusantan El Rufai Sun Koma wajen Uba Sani a APC

  • Wasu makusantan Nasiru El-Rufai sun koma APC tare da nuna goyon bayan Gwamna Uba Sani gabanin zaɓen 2027
  • Daga cikinsu akwai tsohon shugaban ma’aikatan El-Rufai, Bashir Saidu, da tsohon kwamishina kuma tsohon Sanata Abdu Kwari
  • Wannan sauyin sheƙa na iya ƙara ƙarfafa matsayin Gwamna Uba Sani a cikin APC yayin da ’yan siyasa ke shirin zaɓen 2027 da ake tunkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Wasu daga cikin makusanta da masu goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, sun koma jam’iyyar APC tare da bayyana goyon bayansu ga Gwamna mai ci, Sanata Uba Sani, gabanin babban zaɓen 2027.

Rahotanni sun ce ’yan siyasar sun shiga sahun masu goyon bayan tsarin siyasar Uba Sani a jihar, lamarin da zai iya ƙara masa ƙarfi a cikin APC yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Na kusa da El-Rufai sun koma APC
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Makusantan El-Rufai sun sauya sheka

Daga cikin waɗanda aka ce sun koma APC akwai Bashir Saidu, wanda ya taɓa zama shugaban ma’aikatan El-Rufai, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Haka kuma, Abdu Kwari, tsohon kwamishina a jihar kuma tsohon Sanata, na cikin ’yan siyasar da aka ce sun shiga sabon tsarin siyasar Uba Sani.

Sauran sun haɗa da Nasir Abdullahi Maikano, tsohon shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a Kaduna, wanda ya taɓa wakiltar mazaɓar Ungwan Sanusi a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna har sau uku.

An kuma ambaci Moukhtar Isa Hazo, tsohon mataimakin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, da kuma wasu ’yan siyasar daga sassa daban-daban na jihar.

An tabbatar da sauyin sheƙar

Tsohon kwamishinan Kaduna, Jafaru Ibrahim Sani, ya tabbatar da faruwar sauyin siyasar. Ya ce ’yan siyasar sun yanke shawarar tafiya tare domin shiga sabon tsarin.

“Gaskiya ne, za mu tafi tare da su,” in ji shi.

Sauyin na faruwa gabanin zaɓen 2027

Kara karanta wannan

Kurunkus: Tinubu, Atiku da Peter Obi sun bayyana hanyar da suka samu dukiyoyinsu

Wannan sauyin siyasa ya zo ne a daidai lokacin da ake samun sabbin kawance-kawance da sauye-sauyen sheƙa a Jihar Kaduna gabanin zaɓen 2027.

Wasu daga cikin waɗanda aka ambata sun kasance masu alaƙa da tsarin siyasar El-Rufai a lokuta daban-daban, abin da ya sa komawarsu ga APC da goyon bayan Uba Sani ya zama abin lura a siyasar jihar.

Ana sa ran ci gaban zai ƙara haifar da muhawara a Kaduna, yayin da ’yan siyasa daga sansanonin daban-daban ke kokarin ƙarfafa matsayinsu gabanin zaɓen 2027.

Haka kuma, sauyin na iya nuna cewa ana samun sauye-sauye a ma’aunin ƙarfin siyasa tsakanin sansanonin da ke fafatawa a cikin APC da wajen jam’iyyar a jihar.

Jafaru Sani ya koma APC
Malam Jafaru Sani da ya tsallaka zuwa APC Hoto: @JafaruSani01
Source: Twitter

Lauyoyin El-Rufai sun nemi diyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa lauyoyin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun nemi diyyar N10 biliyan daga Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya).

Lauyoyin na tsohon gwamnan jihar Kaduna sun bukaci diyyar ne bisa zargin ɓata sunan wanda suke wakilta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng