Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fadi Abin da Zai Yi wa Tinubu idan Ya Ci Zaben 2027

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fadi Abin da Zai Yi wa Tinubu idan Ya Ci Zaben 2027

  • Ɗan takarar SDP, Adewole Adebayo, ya ce ya fahimci matsalolin da Najeriya ke ciki da kuma kura-kuran da yake ganin gwamnatin Tinubu ta yi
  • Adebayo ya ce duk wanda ya karɓi mulki dole ya ɗauki alhakin nasarori da matsalolin da ya gada daga gwamnatin da ta gabata
  • Ɗan takarar SDP ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan ci gaba da ayyukan gwamnati maimakon ɓata lokaci wajen zargin wanda ya gabace shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, ya ce ya san kura-kuran gwamnatin Bola Tinubu, amma ba zai zarge shi ba idan ya gaje shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Adebayo ya ce ya fahimci ƙalubalen da ke addabar Najeriya da kuma wasu manufofin gwamnatin Tinubu da yake ganin ba su dace ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ware gwamna a Arewa ya kwararo masa yabo

Adebayo ba zai zargi Tinubu ba
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Adewole Adebayo Hoto: Bayo Onanuga, Prince Adewole Adebayo
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Adewole Adebayo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Politics On Sunday na gidan talabijin na TVC.

Sai dai ya jaddada cewa duk wanda ya karɓi mulkin ƙasa dole ne ya amince da nasarorin da ya gada, tare da ɗaukar alhakin matsalolin da suka biyo bayan gwamnatin da ta gabata.

“Lokacin da na zama shugaban ƙasa, da yardar Allah, ba zan zargi Shugaba Tinubu ba. Da zarar an rantsar da ni a matsayin shugaban ƙasa, zan gaji duk abin da shugaban da ya gabace ni ya yi,” in ji Adebayo.

Ya ce zai gaji nasarori da matsaloli

A cewar Adebayo, karɓar alhakin ababen more rayuwa da cibiyoyin gwamnati da aka gada daga tsohuwar gwamnati yana nufin karɓar matsalolin da suka zo tare da su.

Ya ce idan ya shiga gidan gwamnati da wani ya gina, ya yi amfani da hanyar da wani ya gina, ko ya halarci bikin yaye ɗalibai a jami’ar da ba shi ne ya kafa ba, to dole ya amince da abubuwan da ya gada.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya

“Idan zan shiga gidan gwamnati da ba ni na gina ba, na yi amfani da hanyar da ba ni na gina ba, sannan na je bikin yaye ɗalibai a jami’o’in da ba ni na kafa ba, hakan na nufin wanda ya gabace ni ya bar wasu kadarori,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa idan tsohuwar gwamnati ta bar wasu nauye-nauye ko matsaloli, dole ne wanda ya karɓi mulki ya san su kuma ya shirya fuskantar su.

Adebayo ya ce ya san halin tattalin arziki

Ɗan takarar SDP ya ce yana sane da mawuyacin halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki da kuma matsalolin da ke addabar ƙasar, amma duk da haka ya kuduri aniyar neman shugabancin ƙasa.

“A yanzu, na san irin mawuyacin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki. Na san irin halin da Najeriya ke ciki,” in ji shi.

Adebayo ya kuma yi ikirarin cewa ya san kusan dukkanin wuraren da yake ganin gwamnatin Tinubu ta yi kuskure.

“Na san kashi 99 cikin 100 na abubuwan da Shugaba Tinubu ke yi ba daidai ba. Na san su, kuma har yanzu na ƙuduri aniyar neman wannan kujera,” in ji Adebayo.

Ya fi son ci gaba da gwamnati

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa zai mayar da litar fetur N200, ya fadi abin da ya shirya

Adebayo ya ce tsarin mulkinsa ba zai kasance na yawan dora laifi kan wanda ya gabace shi ba, domin zai fi mayar da hankali kan ci gaba da tafiyar da gwamnati.

Ya ce akwai tsarin mika mulki daga wata gwamnati zuwa wata, don haka sabon shugaban ƙasa ba zai iya ware kansa daga abubuwan da ya gada ba.

“Don haka ba zan shiga gwamnati in fara zarginsa ba. Na san duk abin da yake da matsala a cikin gwamnati, kuma akwai tsarin mika mulki. Akwai ci gaba da tafiyar da gwamnati,” in ji shi.
Adewole ba zai ga laifin Tinubu ba
Adewole Adebayo na jawabi a wajen taro Hoto: Prince Adewole Adebayo
Source: Twitter

Adebayo ya yi magana kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Adewole Adebayo ya zargi wasu jami’an gwamnati da haɗa kai da ’yan bindiga wajen ci gaba da matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng