Yadda Dangote Ya Yi Shekara 36 Yana Zaune a Gida 1 ba Tare da Sauya Shi ba
- Hamshakin attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya shafe shekaru 36 yana zaune a gidansa na yanzu kuma ba ya shirin barin gidan
- Dangote ya ce yana jin dadin zama a gidansa, don haka ba ya ganin bukatar neman wani sabon gida ko wasu abubuwan jin dadi na daban
- Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni a Afirka da su fi mayar da dukiyoyinsu wajen kafa masana'antu maimakon abubuwan more rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, ya bayyana cewa ya shafe shekaru 36 yana zaune a gidansa na yanzu kuma ba ya shirin komawa wani gida.
Dangote ya bayyana haka ne yayin da rahotanni suka nuna cewa dukiyarsa ta yi mugun karuwa bayan fara sayar da hannun jarin matatarsa.

Kara karanta wannan
"Ba na son a kara kira na wanda ya fi kowa kudi a Afrika"; Dangote ya fadi sunan da yake so

Source: Getty Images
Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da Arise News ranar Talata, inda ya yi magana kan salon rayuwarsa, harkokin kasuwancinsa da yadda yake kallon arziki da zuba jari.
Gidan da Dangote ke zaune
Rahoton Vanguard ya nuna cewa Dangote ya ce ya dade sosai yana zaune a gidansa na yanzu, kuma yana jin dadin zama a wurin.
Ya ce:
“Kun san tsawon lokacin da na yi a nan? Shekaru 36. Ba na shirin barin wurin. Ina jin dadi sosai a nan.”
Attajirin ya ce gaba daya ya wadatu da gidansa kuma ba ya ganin bukatar ci gaba da neman sababbin abubuwan jin dadi.
Ya kara da cewa:
“Da zarar na shigo gida da yamma, yana da wahala a fitar da ni daga gidana.”
Batun masu sayen jiragen sama
Dangote ya kuma soki wasu masu hannu da shuni a Afirka da ke sayen jiragen sama masu zaman kansu ba tare da zuba jari a masana'antu da sauran harkokin da ke bunkasa tattalin arziki ba.
Ya ce wasu attajirai suna da jiragen sama da yawa kuma suna yawan yawo da su, amma ba su da ko masana'anta guda daya.
Dangote ya ce irin wannan salon kashe dukiya ba ya taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin Afirka, don haka akwai bukatar a sauya wannan dabi'a.

Source: Facebook
Attajirin ya ce babban abin da ya fi ba shi muhimmanci shi ne yin amfani da dukiyarsa da harkokin kasuwancinsa wajen taimakawa wajen bunkasa masana'antu a Afirka.
Ya ce babban abin da yake son a tuna da shi shi ne yadda ya taimaka wajen gina karfin samar da kayayyaki da masana'antu a nahiyar Afrika.
Arzikin Dangote ya karu sosai
A wani labarin, kun ji cewa dukiyar Aliko Dangote ta karu da $19.9bn zuwa $51.3bn bayan fara sayar da hannayen jarin matatar Dangote a kasuwar hannayen jari.
Bayanan Forbes sun nuna cewa dukiyar Dangote ta karu da kashi 63.37 cikin 100 daga $31.4bn zuwa $51.3bn a tsakanin Lahadi da Litinin.
Karin kudin ya daga matsayin Dangote a jerin attajiran duniya na Forbes daga matsayi na 76 zuwa na 36, yayin da matatar Dangote ke neman N2.15trn domin tallafa wa shirin fadada ayyukanta.
Asali: Legit.ng
