Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kawo Sabon Tsarin Tallafi da Zai Taimaki 'Yan Najeriya

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kawo Sabon Tsarin Tallafi da Zai Taimaki 'Yan Najeriya

  • Chukwuemeka Nwajiuba ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta taimaka wa ’yan Najeriya wajen biyan kuɗin wutar lantarki da man fetur
  • Tsohon ƙaramin ministan ilimi ya ce tallafin zai kasance ga ’yan ƙasa kai tsaye, ba kayayyaki ba, yayin da su kuma za su ci gaba da biyan kuɗin ayyukan
  • Nwajiuba ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na LPP ba tare da hamayya ba, yayin da jam’iyyar ta ce za ta fafata a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Liberation People’s Party (LPP), Chukwuemeka Nwajiuba, ya gabatar da wani tsari da zai bai wa gwamnatin Najeriya damar rage wa ’yan ƙasa nauyin kuɗin wutar lantarki da man fetur.

Nwajiuba, wanda tsohon ƙaramin ministan ilimi ne, ya bayyana shirin ne ranar Asabar, 12 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000

Nwajiuba zai samar da tallafi ga 'yan Najeriya
Emeka Nwajiuba da ke neman shugabancin Najeriya a 2027 Hoto: Emeka Nwajiuba
Source: Facebook

Nwajiuba ya yi magana ne yayin da yake karɓar tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban taronta da zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Abuja, cewar rahoton Daily Trust.

Nwajiuba ya ce 'yan kasa za a ba tallafi

Tsohon ministan ya ce bai kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen tallafa wa kayayyaki kai tsaye ba, sai dai ta tallafa wa ’yan ƙasar da ke amfani da su.

Ya ce a tsarin da yake son aiwatarwa, ’yan Najeriya za su ci gaba da biyan kuɗin ayyuka kamar wutar lantarki da man fetur, amma gwamnati za ta taimaka wajen biyan wani ɓangare na kuɗin.

“Ba na son na tallafa wa wani kaya. Mutanen da nake son tallafawa su ne ’yan Najeriya. Ina son na tallafa wa ƙasata,” in ji Nwajiuba.

Gwamnati za ta taimaka wajen biyan kuɗi

Nwajiuba ya bayyana yadda tsarin zai kasance idan aka samu nasarar aiwatar da shi.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Tinubu, Atiku da Peter Obi sun bayyana hanyar da suka samu dukiyoyinsu

Ya ce idan ɗan ƙasa ya biya kuɗin wutar lantarki, gwamnati za ta taimaka masa wajen biyan kuɗin, amma dole ne shi ma ya biya wani ɓangare.

Haka kuma, ya ce masu sayen man fetur za su biya kuɗinsa, yayin da gwamnati za ta taimaka wajen rage musu nauyin kuɗin.

LPP za ta gina tsarinta kafin zaɓen 2027

Nwajiuba ya kuma ce jam’iyyar LPP ta kammala gudanar da tarukanta na ƙananan hukumomi da sauran matakan cikin gida, kuma za ta kafa cikakkun tsare-tsare a dukkan unguwanni gabanin zaɓen 2027.

Ya samu matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ba tare da hamayya ba a babban taron da aka gudanar a Abuja.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abubakar Ishaq Dogara, ya ce fitowar Nwajiuba a matsayin ɗan takara ta nuna sabon shafi a tarihin LPP.

Dogara ya ce jam’iyyar na da tsari a dukkan jihohi 36 da kuma Abuja, kuma za ta fafata a zaɓen shugaban ƙasa da sauran kujerun zaɓe a 2027.

Nwajiuba ya yi wa yan Najeriya alkawari
Emeka Nwajiuba na magana a wajen taro Hoto: Emeka Nwajiuba
Source: UGC

Sowore ya yi wa ma'aikata alkawarin N500,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi alkawarin samar da mafi ƙarancin albashin N500,000 duk wata ga ma’aikata.

Sowore, wanda ɗan gwagwarmaya ne, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin AAC za ta samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24 a Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng