INEC Ta Bayyana Jam'iyyu 6 da Za Su Fafata a Zaben Cike Gurbin Dan Majalisa a Kano

INEC Ta Bayyana Jam'iyyu 6 da Za Su Fafata a Zaben Cike Gurbin Dan Majalisa a Kano

  • Jam’iyyu shida ne za su fafata a zaben cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazabar Dawakin Kudu ranar Asabar mai zuwa
  • Hukumr INEC za ta tura ma’aikatan wucin gadi 1,500 zuwa rumfunan zabe 303 a fadin mazabar
  • Bayanai sun nunbacewa mazabar tana da masu kada kuri’a 162,445, yayin da aka karbi katunan zabe, PVC 148,971

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce jam’iyyun siyasa shida ne za su fafata a zaben cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazabar Dawakin Kudu da za a gudanar ranar Asabar.

Kwamishinan zaɓe na INEC a Kano, Abdu Zango, ne ya tabbatar da hakan ranar Talata bayan taron Kwamitin Tuntuba na Tsaro kan Zabe.

INEC.
Tambarin hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa taron ya gudana ne tsakanin shugabannin hukumomin tsaro a hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Matsala ga Tinubu: Ana ganin Atiku zai lashe jihohi 19 a Arewa da 3 a Kudu a zaben 2027

INEC za ta tura ma'aikatan wucin gadi

Zango ya ce hukumar za ta tura ma’aikatan wucin gadi 1,500 zuwa rumfunan zabe 303, inda ya kara da cewa an riga an rarraba kayayyakin zabe marasa muhimmanci, yayin da za a kawo kayayyakin zabe masu muhimmanci ranar Laraba mai zuwa.

Ya ce dukkan hukumomin INEC da na tsaro sun tabbatar wa mazauna yankin cewa zaben zai kasance cikin kwanciyar hankali, ’yanci da adalci.

“Duk zabe darasi ne. Mun taba gudanar da zabe a Dawakin Kudu a baya kuma ya kasance cikin ’yanci, adalci, sahihanci da zaman lafiya. Babu wata matsala ko kadan. Za mu sake yin hakan, har ma fiye da baya,” in ji Zango.

Dakarun ‘yan sanda sun shirya

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tura jami’an tsaro zuwa wuraren zabe zai fara ne daga ranar Alhamis.

“Mun shirya tsaf kuma za mu fara tura jami’an tsaro daga ranar Alhamis. Zaben zai kasance cikin zaman lafiya, adalci da ’yanci, mun shirya tsaf.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 400 da za su yi wa APC, ADC, NDC da PDP takarar sanatoci a 2027

"A ko da yaushe ana samun ci gaba a kowane tsari, kuma tabbas an samu ci gaba daga abin da muka yi a baya,” in ji shi.
Amuoitan.
Shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

An shirya gudanar da zaben cike gurbin ne bayan kujerar ta zama babu kowa sakamakon tsohon dan majalisar ya koma Majalisar Wakilai ta Tarayya.

INEC ta bayyana a baya cewa mazabar tana da masu kada kuri’a 162,445 da suka yi rajista, yayin da mutane 148,971 suka karbi katunan zabe na dindindin (PVC), wanda ke wakiltar kashi 91.7 cikin 100 na yawan wadanda suka yi rajista.

INEC ta fitar da sunayen yan takara

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fitar da jerin ’yan takarar shugaban ƙasa na karshe da za su fafata a babban zaben 2027.

Jerin, wanda Rose Oriaran-Anthony, Sakatariyar Hukumar INEC, ta sanya wa hannu, ya ƙunshi jam’iyyun siyasa 18 da ’ yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262