Dan Sheikh Nuru Khalid da Ya Koma Kiristanci Ya Dawo Musulunci, Ya Yi Bayanai

Dan Sheikh Nuru Khalid da Ya Koma Kiristanci Ya Dawo Musulunci, Ya Yi Bayanai

  • A kwanakin baya yaron Sheikh Nuru Khalid ya sanar da cewa ya sauya addini daga musulunci zuwa kiristanci bayan ya yi bincike
  • Ibrahim Nuru Khalid ya fitar da sabon bidiyo inda ya tabbatar da cewa ya dawo cikin addinin musulunci kuma ya bar kiristancin da ya koma a baya
  • Yaron na fitaccen malamin addinin musuluncin ya nemi gafarar al'ummar musulmai tare da neman su sanya shi cikin addu'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - 'D a ga fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Nuru Khalid ya dawo cikin addininsa na asali bayan ya koma kiristanci.

Ibrahim Nuru Khalid ya sanar da cewa a yanzu ya dawo cikin addinin musulunci bayan a kwanakin baya ya fice daga cikinsa.

Yaron Nuru Khalid ya dawo musulunci
Ibrahim Nuru Khalid na gabatar da jawabi Hoto: Sheikh Muhammad Nuru Khalid
Source: Facebook

Yaron na fitaccen malamin ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da yake magana a cikin wanda aka fitar a shafin Facebook, ranar Talata, 15 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Babban malami a Najeriya ya zargi wasu mutane da daukar nauyin 'yan bindiga, ya faɗi dalili

Ibrahim Nuru Khalid ya taba barin musulunci

A kwanakin baya dai Ibrahim Nuru Khalid ya bayyana cewa ya koma cikin addinin Kiristanci bayan ya yi bincike-bincike.

Yaron na fitaccen malamin ya bayyana cewa ya yi duba ga littafi mai tsaki na Al-Kur'ani da bible kafin ya dauki matakin komawa addinin kiristanci.

Sauya addinin na sa dai ya jawo cece-kuce da gutsiri tsoma duba da irin girman da mahaifinsa yake da shi da sunan da ya yi wajen karantarwar addinin musulunci.

Wasu kuma sun rika mamaki kan yadda da ga fitaccen malamin zai dauki matakin komawa wani addini daban ba musulunci ba.

Ya dawo cikin musulunci

A cikin sabon bidiyon da ya fitar, Ibrahim Nuru Khalid ya bayyana cewa ya dawo cikin addinin musulunci.

Ya tabbatar da cewa a kwanakin baya ya yi bidiyo inda ya sanar da ficewarsa daga cikin addinin musulunci zuwa kiristanci.

"Sunana Ibrahim Nuru Khalid, a kwanakin baya na yi bidiyo na sauya addini zuwa kiristanci, amma yanzu Allah ya taimake ni na dawo musulunci. Ina kuma neman gafarar musulmi da su yafe mini game da zargin hadisin Annabi Muhammad da na yi.. Sannan kuma ina neman afuwar Allah a kai."

Kara karanta wannan

'Ya ci mana mutunci': Jigon PDP ya caccaki Farfesa Pantami kan siyasa

"Ina mai ba da hakuri ga al'ummar musulmai game da wannan kaddara da ta same ni, sannan kuma ina neman addu'ar musulmai gabakidaya domin Allah ya taimake ni na tsaya cikin musulunci tun da dama ni musulmi ne na fita daga ciki." In ji shi

Ibrahim Nuru Khalid ya kuma tabo batun rashin lafiyar da mahaifinsa ya ce yana fama da ita, inda ya ce ya fi kowa cancanta ys yi magana a kansa.

Ibrahim Nuru Khalid ya bar kiristanci
Ibrahim Nuru Khalid da ya dawo musulunci Hoto: Sheikh Muhammad Nuru Khalid
Source: Facebook

An kori Nuru Khalid daga limanci

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kwamitin jagorancin masallacin rukunin gidajen yan majalisu da ke unguwar Apo a birnin tarayya Abuja, ya kori Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Masallacin.

Korar da kwamitin masallacin ya yi wa malamin addinin musuluncin ta biyo bayan wanj zazzafan wa'azi da ya yi kan matsalar tsaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng