Murtala Asada Ya Caccaki Gwamnatin Sokoto kan Rufe Masallacin Sheikh Lukuwa
- Malam Murtala Bello Asada ya yi Allah-wadai da matakin gwamnatin jihar Sokoto na rufe masallacin Juma'a na Sheikh Musa Lukuwa
- Asada ya zargi gwamnatin da neman siyasantar da matsalar addini da kuma amfani da sunan Manzon Allah (SAW) wajen yaudara
- Malamin ya bayyana cewa gwada gudanar da bincike ta hanyar malamai kuskure ne, ya kamata a haɗa ɓangarorin biyu su yi muƙabala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sokoto – Malam Murtala Bello Asada ya fito ya nuna adawarsa da kuma sukar matakin da gwamnatin jihar Sokoto ta ɗauka biyo bayan rikicin da ya ɓulla a masallacin Sheikh Musa Ayuba Lukuwa.
Malamin ya bayyana cewa irin matakan da gwamnatin ke shirin ɗauka sune yunƙurin siyasantar da al'amuran addini da kuma yin amfani da hanyoyin yaudara.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook, Murtala Asada ya yi tir da salon da gwamnatin jihar ta bi wajen gudanar da al'amarin, inda ya ce an riga an yanke hukunci domin kawai a faranta wa wadansu rai.
Ya rubuta cewa:
"Mun yi Allah-wadai da kuma tir da irin ƙoƙarin siyasantar da matsalar addini da gwamnatin jihar Sokoto take shirin aikatawa.
"Acikin takardar da gwamnatin ta fitar wadda take ƙunshe da yaudara, makirci da kuma ƙoƙarin yin siyasa da sunan Manzon Allah (SAW), inda take cewa: ta nisanta kanta daga duk wani mai fakewa da addini yana cin mutuncin Manzon Allah (SAW).
"Wannan ƙarya ce, kuma wannan ya nuna cewa gwamnati ta riga ta yanke hukunci don ta faranta wa jahilai."
Malam Murtala Asada ya ƙara da cewa kafa kwamitin malamai domin gudanar da bincike yaudara ce kawai saboda bincike ba aikin malamai ba ne.
Matakin da ya dace a ɗauka
A cewarsa, abin da ya kamata gwamnati mai adalci ta yi shi ne haɗa ɓangarorin biyu domin gudanar da muƙabala a kan abin da ya faɗa don ya ƙare kansa.
"Duk wata gwamnati mai hankali da adalci idan aka samu jayayya tsakanin ɓangarori guda biyu, to haɗa su take yi su yi karatu, sai kowa ya kawo hujjarsa, sai kuma a saka wasu malamai su yi alƙalanci,
"Waɗanda ba su da alaƙa da kowane ɓangare. Amma abin mamaki wai wanda aka kawo wa hari ya ƙare kansa, wai kuma shi ne za a tuhuma tare da rufe masa masallaci."

Source: Original
Asada ya jaddada cewa wannan mataki ya fito da ɓoyayyar manufa a fili cewa an tsara rikicin ne tun farko domin maƙasudin siyasa.
Matakin da gwamnatin Sokoto ta ɗauka
A wani labarin daban, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta ba da umarnin rufe masallacin Juma'a na Sheikh Musa Ayuba Lukuwa da ke yankin Mabera.
Wannan mataki ya biyo bayan zargi a kan harin da aka kai wa malamin da kuma kashe mutumin da ake zargi da kai harin bayan kammala sallar Juma'a.
Gwamnatin ta nemi a gudanar da bincike mai zurfi tare da kafa kwamitin malamai na musamman domin samar da shawarwari kan yadda za a murƙushe matsalar.
Asali: Legit.ng


