Ba kamar Tinubu ba, Peter Obi Ya Yi Ta Maza da Aka Nemi a Saki Takardun Karatunsa

Ba kamar Tinubu ba, Peter Obi Ya Yi Ta Maza da Aka Nemi a Saki Takardun Karatunsa

  • Peter Obi ya ce ba shi da wata matsala da Jami’ar Najeriya da ke Nsukka ta fitar da takardun digirinsa da sauran bayanan karatunsa
  • Obi ya ce jami’ar ta ba shi digirin BA a Falsafa a shekarar 1984, kuma ya nemi a fitar da bayanan bisa doka idan an yi buƙatar hakan
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC ya ce ya yi amanna da gaskiya da riƙon amana, amma ya buƙaci a gudanar da binciken tarihin ’yan takara cikin adalci da bin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya nemi Jami’ar UNN da ke Nsukka ta fitar da bayanan karatunsa.

Peter Obi ya bukaci hakan ne bayan rahotannin daukar matakin shari’a da ke neman kwafin takardun karatunsa.

Kara karanta wannan

Ko da tsiya tsiya: ADC ta bayyana shirinta kan zaben 2027

Obi ya amince a saki takardun karatunsa
Peter Obi na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 15 ga watan Satumban 2026.

Ya ce ba shi da wata matsala da a fitar da takardun digirinsa da sauran bayanan da suka shafi karatunsa a jami’ar.

Obi ya ce ya karɓi digirin Falsafa a 1984

Peter Obi ya ce Jami’ar Najeriya ta ba shi digirin Bachelor of Arts (BA) a fannin Falsafa a shekarar 1984.

Sanarwar tasa ta biyo bayan yaɗuwar rahotanni a kafafen sada zumunta game da wani mutum ko rukuni da ya ɗauki matakin shari’a domin neman kwafin takardar digirinsa da wasu bayanan da suka shafi karatunsa.

Obi ya ce ba shi da wata matsala kan fitar da waɗannan takardu.

“Ina son na bayyana karara cewa ba ni da wata adawa ko kaɗan da fitar da waɗannan bayanai,” in ji shi.

Ya nemi jami’ar ta fitar da bayanan bisa doka

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya shiga maganar Sanata Shehu Buba da ake zargi da ta'addanci

Tsohon gwamnan na Anambra ya buƙaci Jami’ar UNN da ke Nsukka ta samar da takardun shaidar karatunsa, bayanansa da sauran takardun da suka shafi shigarsa jami’a da karatunsa, matuƙar an yi buƙatar hakan ta hanyar da doka ta amince da ita.

Ya kuma ce ba shi da wata adawa da hakan a sauran makarantun da ya halarta, a Najeriya da wajen ƙasar, kan su fitar da bayanan karatunsa bisa dokoki da ƙa’idojin da suka dace.

Obi ya ce yana maraba da binciken tarihinsa

Obi ya bayyana cewa ya yi imani sosai da gaskiya da riƙon amana, musamman ga mutanen da ke neman riƙe mukamin gwamnati.

Sai dai ya jaddada cewa ya kamata a gudanar da bincike kan ’yan takara cikin adalci, bisa doka kuma ba tare da nuna wariya ba.

Peter Obi ya ce a saki takardun karatunsa
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Peter Obi ya ce bai ki karbar tayin Atiku ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi, ya musanta rahotannin cewa ya ƙi karbar tayin zama abokin takarar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, a zaɓen 2027.

Peter Obi ya ce ba a taɓa yi masa irin wannan tayin ba, don haka ba zai yiwu ya ƙi wata shawara da ba a gabatar masa da ita ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng