Dangote Ya Yi Maganar Samun Yaron da Zai Gaje Shi, Ya Fadi Fatansa kan 'Ya'yansa Mata 3
- Aliko Dangote ya ce ’ya’yansa mata uku, Halima, Fatima da Mariya, duk suna da damar gaje shi wajen jagorantar Dangote Group
- Attajirin ya ce bai tilasta wa ’ya’yansa shiga harkar kasuwancin ba, domin sun shiga ne saboda sha’awarsu kuma suna jin daɗin aikin
- Dangote ya ce babban abin da ya fi damunsa shi ne tabbatar da gudanar da kamfanin cikin ƙwarewa da ingantaccen tsarin shugabanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban Dangote Group, Aliko Dangote, ya ce samun ɗa namiji da zai gaji daular kasuwancinsa ba shi ne babban abin da ya fi ba shi muhimmanci ba.
Dangote ya ce ’ya’yansa mata uku, Halima, Fatima da Mariya, suna da ƙwarewar da za ta ba su damar jagorantar babbar daular kasuwancin Dangote Group a nan gaba.

Source: Getty Images
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News ranar Talata, 15 ga watan Satumban 2026.
“Ɗaya daga cikinsu za ta iya jagoranci”
Da aka tambaye shi ko yana ganin ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata za ta iya karɓar ragamar kamfanin, Dangote ya ce yana ganin hakan zai yiwu.
“Ina ganin eh, ina ganin ɗaya daga cikinsu za ta iya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ya daɗe yana kallon yadda ’ya’yansa mata ke gudanar da ayyukansu, kuma yana ganin ɗaya daga cikin ukun za ta iya jagorantar rukunin kamfanonin.
Halima, Fatima da Mariya suna riƙe da manyan muƙamai a cikin rukunin kamfanonin, yayin da ayyukansu ke ƙara faɗaɗa a daidai lokacin da kamfanin ke gina tsarin maye gurbin shugabanci.
’Ya’yansa sun shiga kasuwanci ne da son ransu
Dangote ya ce shigar ’ya’yansa cikin harkar kasuwancin ba ta faru ne saboda matsin lamba daga gare shi ba. Ya ce dukkansu suna da sha’awar kasuwancin sosai kuma suna jin daɗin aikin da suke yi.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya kawo sabon tsarin tallafi da zai taimaki 'yan Najeriya
“Suna da matuƙar sha’awar kasuwancin. Ba na tilasta musu su zo su kasance cikin wannan kasuwanci ba. Suna da sha’awa sosai kuma suna jin daɗinsa,” in ji shi.
Ya ce ’ya’yansa mata za su iya zarce shi
Attajirin kuma wanda ya fi kowa arziki a Afirka ya ce yana ganin ’ya’yansa mata za su iya yin abin da ya fi nasarorin da ya samu tare da kai kamfanin zuwa wani sabon matsayi.
Dangote ya ce ’ya’yansa mata sun samu ingantaccen ilimi, wanda zai taimaka musu wajen samar da sababbin dabaru a harkokin kasuwanci.
“Ɗaya daga cikinsu na iya yin abin da ya fi nawa. Ban taɓa tsammanin zan kai wannan matakin ba,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko yana ganin duka ’ya’yansa mata ukun za su iya cimma hakan, Dangote ya amsa da cewa: “Dukkansu.”
Dangote ya yi maganar samun ɗa namiji
Da aka tambaye shi ko har yanzu yana fatan samun ɗa namiji, musamman ganin irin muhimmancin da al’adar Kano ke bai wa ɗa namiji wajen gado, Dangote ya ce hakan ba fifikonsa ba ne.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
“Wannan, ina ganin, ba shi ne abin da na fi ba muhimmanci ba,” in ji shi.
Ya ce samun ɗa namiji ba lallai ne ya tabbatar da dorewar sunan iyali ko gadon arziki ba.
Dangote ya ce Allah ne ke iko da komai, yana mai cewa wani lokaci mutum na iya roƙon Allah ya ba shi ɗa namiji, amma daga baya ɗan ya zama wanda zai lalata sunan iyalinsa.
“Wani lokaci idan Allah bai ba ka wani abu ba, kada ka matsa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ko da yana da ɗa namiji, bai yi imanin cewa ɗan zai iya yin abin da ya fi ’ya’yansa mata ukun ba.

Source: Getty Images
Dangote ya dade a gidansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Aliko Dangote ya bayyana cewa ya shafe shekaru 36 yana zaune a gidansa kuma ba ya shirin komawa wani gida.
Attajirin ya ce gaba daya ya wadatu da gidansa kuma ba ya ganin bukatar ci gaba da neman sababbin abubuwan jin dadi.
Asali: Legit.ng
