Magana Ta Kare, INEC Ya Fitar da Sunayen Yan Takarar Shugaban Kasa na Karshe kafin Zaben 2027
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fitar da jerin ’yan takarar shugaban ƙasa na karshe da za su fafata a babban zaben 2027
- Jam’iyyu 18 ne suka bayyana ’yan takararsu da mataimakansu kuma sunayensu sun isa ga hukumar INEC kamar yadda doka ta tanada
- Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima za su sake neman kujerar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa da aka tsara gudanarwa a watan Janairun 2027.
Jerin, wanda Rose Oriaran-Anthony, Sakatariyar Hukumar INEC, ta sanya wa hannu, ya ƙunshi jam’iyyun siyasa 18 da ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu.

Kara karanta wannan
2027: Sanata Yari ya yanke hukunci kan wanda ya cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi

Source: Facebook
Manyan yan takara 3 na sahun gaba
Vanguard ta ruwaito vewa jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da Shugaba Bola Tinubu, mai shekaru 74, a matsayin ɗan takararta, yayin da Kashim Shettima, mai shekaru 59, zai sake kasancewa mataimakinsa.
A gefe guda, African Democratic Congress (ADC) ta tsayar da Atiku Abubakar, mai shekaru 79, tare da Chibuike Rotimi Amaechi, mai shekaru 61, a matsayin mataimakinsa.
Haka kuma, Peter Gregory Obi, mai shekaru 65, na jam'iyyar NDC, zai tsaya takara tare da Sanata Rabiu Kwankwaso, mai shekaru 69 a matsayin mataimakinsa.
Jerin sunayen sauran yan takara 15
Sauran yan takarar shugaban kasa 15 da hukumr INEC ta fitar da sunayensu sun hada da:
- Sunday Chibuzo Okereke (LP) — Hajja Bintu Konto
- Sandy Ojang Onor (PDP) — Umaru Babangida
- Rufai Adekunle Omo-Aje (AA) — Shehu Hussaini
- Aliyu Abbas-Bin (ADP) — Chinazam Ike
- Kabiru Yusuf (APP) — Peace Egobia Ofordile
- Omoyele Sowore (AAC) — Haruna Garba Magashi
- Oluseyi Abiodun Makinde (APM) — Musa Lawal Daura
- Sunday Adenuga (BP) — Usman Turaki Mustapha
- Moses Olusoji Adebisi (DLA) — Nafisat Usaku Abubakar
- Ada Elizabeth Fredrick Okwori (NDP) — Uchenna Anthony Chukwuemeka
- Nkem Esther Okereke (NRM) — Nasir Muhammed Sulaiman
- Donald Duke (PRP) — Kabiru Rabiu
- Adewole Ebenezer Adebayo (SDP) — Usman Muhammed Bugaje
- Peter Ada Agada (YPP) — Patience Ndidi Key
- Daniel Daberechukwu Nwanyanwu (ZLP) — Hassan Khalid
Mata biyu sun tsaya takara a 2027
A cewar takardar, babu wani daga cikin ’yan takarar shugaban ƙasa 18 ko mataimakansu da ya bayyana cewa yana da wata nakasa.
Sai dai jerin ya ƙunshi mata biyu da suka tsaya takarar shugaban ƙasa, wato Ada Elizabeth Fredrick Okwori ta NDP da Nkem Esther Okereke ta NRM.
Haka kuma, akwai mata huɗu da ke takarar mataimakiyar shugaban ƙasa.

Source: Facebook
Shekaru da cancantar karatu
Shekarun ’yan takarar sun fara daga 35 zuwa 80, yayin da matakan karatunsu suka bambanta daga Takardar Kammala Makarantar Firamare, WAEC da NABTEB zuwa digiri na jami’a.
Jerin ya kuma ƙunshi ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu da ke da digirin digirgir.
INEC ta soki shirin Peter Obi
Kun ji cewa INEC ta sake jaddada cewa ita ce kadai ke da ikon tattarawa da sanar da sakamakon zabe yayin da ake shirin zaben 2027.
Wannan na zuwa ne yayin da jam’iyyun adawa ta NDC da Peter Obi ke shirin samar da hanyoyin da za su rika bibiyar sakamakon rumfunan zabe a zabenN2027.
Asali: Legit.ng
