An Fara Rade Radin Kulla Sabuwar Hadaka domin Kifar da Tinubu a 2027

An Fara Rade Radin Kulla Sabuwar Hadaka domin Kifar da Tinubu a 2027

  • Sabuwar alaka tsakanin Peter Obi da Seyi Makinde ta sake farfado da rade-radin kafa kawancen 'yan adawa domin kalubalantar Bola Tinubu a zaben 2027
  • Obi da Makinde, wadanda ba su kasance a bangare daya ba a zaben 2023, an gan su tare a wani taro na sirri a Ibadan, lamarin da ya kara jawo hankali
  • Sai dai manyan tambayoyin da ke gaban 'yan adawar sun hada da ko za su iya hada kai, shawo kan bambance-bambancen jam'iyyu da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Kara kusanci tsakanin dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, da Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya sake haifar da rade-radin yiwuwar kafa kawancen 'yan adawa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

An ga shugabannin biyu tare a wani taro na sirri a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sannan suka sake bayyana tare a wasu tarukan jama'a.

Kara karanta wannan

Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

Peter Obi da wasu 'yan adawa
Yadda Peter Obi ya je wajen taron APM. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Twitter

Alakar Obi da Makinde

Vanguard ta wallafa cewa Obi ya halarci bikin bude ofishin yakin neman zaben Makinde na jam'iyyar APM a Abuja a ranar Litinin din da ta gabata.

Makinde ne dan takarar shugaban kasa na APM a zaben 2027, abin da ya sa bayyanar Obi a wajen bude ofishin nasa ta dauki hankalin 'yan siyasa.

Wannan shi ne karo na farko a baya-bayan nan da aka ga dan takarar shugaban kasa yana halartar bude ofishin yakin neman zaben wani dan takarar da zai fafata da shi.

Majiyoyi na kusa da bangarorin biyu sun ce tattaunawarsu ta mayar da hankali kan maslahar kasa, shugabanci da kuma dabarun siyasar zaben 2027.

Obi da Makinde sun rabu a 2023

A zaben 2023, Makinde, wanda a lokacin yake cikin manyan jiga-jigan PDP, yana daga cikin gwamnonin G-5 da suka yi adawa da burin Atiku Abubakar na neman shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

2027: An samu babbar matsala a yunkurin fitar da ɗan Takara 1 tsakanin Atiku, Peter Obi da Makinde

A daya bangaren kuma, Obi ya jagoranci jam'iyyar LP a wani gagarumin yakin neman zabe da ya samar da wata babbar rundunar magoya baya da aka fi sani da "Obidient".

Sai dai sauye-sauyen siyasa da suka biyo bayan zaben 2023 sun sa Makinde ya fara nuna matsaya mai zaman kanta, tare da sukar wasu manufofin gwamnatin tarayya da kuma kira ga hadin kan 'yan adawa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kalubalen da ke gabansu

Rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP ya kara sauya yanayin siyasar Makinde, wanda daga bisani ya koma APM domin neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar.

Obi kuma ya ci gaba da hada kan magoya bayansa karkashin kungiyar "Obidient", yayin da bai kawar da yiwuwar sake neman shugabancin kasa ba.

Ana tambayar ko Obi da Makinde za su iya zama ginshikin wata babbar kungiyar adawa da za ta hada wasu daga cikin 'yan PDP da ba na bangaren Wike ba, LP, NNPP, ADC da sauran kungiyoyi.

Haka kuma akwai tambayar ko shugabannin adawar za su iya ajiye bambance-bambancen kansu, na yanki da na jam'iyya domin samar da matsaya guda gabanin zaben.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

Obi da Makinde sun rage muhimmancin rade-radin cewa sun kulla kawance na siyasa, inda suke bayyana ganawarsu a matsayin "tattaunawar masu kishin kasa".

Kira a zabi Tinubu a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya yi kira ga al'ummar Arewa da su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaben shugaban kasa a 2027.

Buni ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin wani taron kungiyar malamai ta shirya tare da hadin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Kabiru Masari.

Gwamnan ya ce idan Arewa ta samu damar mulki na tsawon shekaru 8 karkashin shugaban da ya yi wa'adi biyu, to adalci da gaskiya sun nuna ya kamata a bai wa Tinubu damar yin wa'adi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng