Bamanga Tukur: Tarihi da Rayuwar Shugaban Jam’iyyar PDP na kusan Karshe a Mulki
Adamawa - A ranar Lahadi 13 ga watan Satumba 2026 aka birne Bamanga Tukur a babban Masallaci na Modibbo Adama a Yola.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
An yi wa marigayin sallah ne a masallacin da yake babban birnin jihar Adamawa kuma daga nan ake birne shi a filin gidan dangi.

Source: UGC
Jana'izar Alhaji Bamanga Tukur a Yola
Rahotanni sun gabata cewa an rufe Bamanga Tukur a Aunguwar Sanda da ke birnin Yola a ranar.
Baya ga Mai girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da jami’an gwamnati da ‘yan siyasar Adamawa, manya sun halarci jana’izar.
Mahalartan sallar sun hada da Lamidon Adamawa, Barkindo Aliyu Musdafa; Aliko Dangote; Sanata Iya Abbas da Jibrilla Bindow.
Rahoton nan daga Daily Trust ya tattaro wasu abubuwa game da rayuwar marigayi Bamanga Tukur.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu
Bamanga Tukur ya yi aiki a tashoshin ruwa, kamfanoni da kuma fagen siyasa a lokacin mulkin sojoji da na farar hula a Najeriya.
Haihuwa da karatun Bamanga Tukur a kasar waje
An haife shi ne a ranar 15 ga watan Satumba 1935, ya bar duniya ne daf da ranar haihuwarsa, yana mai shirin cika shekara 91.
Yana matashi ya halarci makarantar London School of Economics a Ingila, ya karanta ilmin sufuri da tattalin arziki a shekarar 1965.
Daga baya ya koma jami’ar Pittsburgh a kasar Amurka, ya samu shaidar digirin digir-gir.
Zaman Bamanga shugaban hukumar NPA
Sakamakon haka aka nada shi shugaban hukumar tashoshin ruwa (NPA) a 1975, bai sauka daga matsayin ba sai bayan shekaru bakwai.
Ana cewa a lokacinsa an ga sauyi a harkokin tashohin ruwan Najeriya, wannan ya jawo masa matsayi a Afrika da kasashen duniya.
Takarar gwamnan jihar Gongola a 1983
Lokacin da ya ajiye wannan aiki sai ya shiga harkar siyasa, ya kuma nuna sha’awar neman takarar gwamnan Gongola a zaben 1983.
A jamhuriyya ta biyu, jihar Gongola ta hada jihohin Anambra da Taraba na yau.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Gwamnoni, Malamai da manyan Arewa sun yi taro, sun yiwa Tinubu mubaya'a
Da aka shiga zabe kuwa, Bamanga da ya tsaya takara a jam’iyyar NPN mai mulki ya doke gwamnatin Abubakar Barde ta GNPP.
Kasuwanci da zama minista bayan juyin mulki
Marigayin bai wuce watanni uku kan mulki ba sai sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula a karshen shekarar Disamban 1983.
Ganin Janar Muhammadu Buhari ya yi juyin mulki, sai tsohon gwamnan ya koma harkokin kasuwanci, a nan ya kafa kamfanoni.
Lokacin ya kafa kamfanin BHI Holdings da aka fi sani da DADDO Group of Companies.
Shekaru 10 da yin haka sai aka nada shi Ministan masana’antu lokacin Janar Sani Abacha ya sake yin wani juyin mulki a 1993.
Ya kasance farar hular da suka zama ministoci a gwamnatin sojan har zuwa shekarar 1995.
Dawo wa siyasa da rikicewar PDP a hannun shi
Alhaji Bamanga ya yi yunkurin zama sanata bai dace ba, amma ana dawo wa mulkin farar hula da kyau a 1999 suka kafa jam’iyyar PDP.
Sai a 2012 aka jawo shi ya zama shugaban PDP na kasa. Wa’adin da ya cika da rikicin cikin gida har ya yi murabus da kan sa a cikin 2014.
Gwamnoni bakwai da ‘yan majalisa fiye da 20 suka balle daga jagorancin Bamanga.
A 2015 Bamanga ya hakura da harkokin siyasa
Adamu Muazu ya canje shi bayan jam’iyyar PDP ta rasa gwamnoni da manyan ‘yan siyasa, a karshe APC ta doke ta a zaben 2015.
Sa’ilin da ya cika shekara 80 a duniya, sai ya sanar da cewa ya hakura da siyasa, ya ba matasa dama su shiga a dama da su da kyau.
A satumban nan ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya ‘ya 18. daga cikinsu akwai wadanda sun yi suna a siyasa da wasu harkokin a yau.
Gwamnan Adamawa a kafar X ya wallafa hotunan sallar jana'izar da aka yi a birnin Yola.
Shugaban kasa ya yi ta'aziyyar Bamanga
Rahoto ya zo cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Bamanga Tukur.
Shugaban kasa ya bayyana marigayin a matsayin babban jigo da ya ba da gudummawa wajen haɓaka kasuwanci, siyasa da ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Iyalan marigayin sun tabbatar da cewa ya rasu ne a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Asabar, 12 ga watan Satumba, 2026.
Asali: Legit.ng
