ADC Ta Aika Sako ga INEC bayan Malaman Jami'a Sun Goyi Bayan Tinubu a 2027

ADC Ta Aika Sako ga INEC bayan Malaman Jami'a Sun Goyi Bayan Tinubu a 2027

  • ADC ta buƙaci INEC ta hana malaman jami’a da aka san suna da ra’ayin siyasa zama jami’an tattara da haɗa sakamakon zaɓen 2027
  • Jam’iyyar ta ce goyon bayan da sama da malaman jami’a 600 suka nuna wa Tinubu na iya haifar da shakku sahihancin wasu jami’an zaɓe
  • ADC ta nemi INEC ta fitar da ƙa’idojin tantance jami’an zaɓe tare da wallafa sunayensu kafin zaɓe domin jama’a da jam’iyyu su duba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta mika sabuwar bukata ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Jam'iyyar ADC ta bukaci hukumar INEC ta hana malaman jami’a da aka san suna da alaƙar siyasa zama jami’an tattara da haɗa sakamakon zaɓen 2027.

ADC ta mika bukatarta ga INEC
Shugabannin ADC a wajen taron jam'iyyar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Jam’iyyar ta bayyana matsayinta ne a wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya bayar da shawara kan mutanen da za a zaba a 2027

ADC ta nuna damuwa kan goyon bayan Tinubu

Sanarwar ta biyo bayan rahotannin cewa sama da manyan malaman jami’a 600 daga jami’o’in gwamnati da ke Arewacin Najeriya sun fito fili sun nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen 2027.

ADC ta ce hakan ya haifar da tambayoyi kan ko wasu daga cikin malaman jami’ar da ake amfani da su a matsayin jami’an zaɓe za su iya gudanar da ayyukansu ba tare da nuna son kai ba.

Jam’iyyar ta ce nada malaman jami’a da suka fito fili suka bayyana matsayinsu na siyasa na iya jefa sahihancin tsarin zaɓe cikin barazana.

Ta kuma ce hakan na iya haifar da rikicin muradu, saboda malamai da shugabannin jami’o’i kan taka muhimmiyar rawa wajen tattara sakamakon zaɓe da sanar da waɗanda suka yi nasara.

’Yan Najeriya na da ’yancin zaɓar ɗan takara

ADC ta amince cewa malaman jami’a, kamar sauran ’yan Najeriya, suna da ’yancin da kundin tsarin mulki ya ba su na mara wa ’yan takarar siyasa baya ko amincewa da su.

Kara karanta wannan

Ko da tsiya tsiya: ADC ta bayyana shirinta kan zaben 2027

Sai dai jam’iyyar ta ce mutanen da suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga wani ɗan takara bai kamata su shiga aikin tattara ko sanar da sakamakon zaɓen da ɗan takarar nasu ke ciki ba.

Jam’iyyar ta ce bai dace mutumin da ya yi wa wani ɗan takara kamfen ya kasance wanda zai ƙirga ƙuri’u ko ya sanar da sakamakon zaɓen da ɗan takarar ke neman nasara ba.

ADC ta nemi INEC ta kafa sabbin ƙa’idoji

Jam’iyyar ta buƙaci INEC ta samar tare da wallafa ƙa’idoji masu bayyana yadda za a hana malaman jami’a da sauran masu neman zama jami’an zaɓe waɗanda suka fito fili suka amince da wani ɗan takara shiga aikin.

A cewar ADC, ya kamata a cire daga cikin waɗanda za a nada duk wanda ya shiga yakin neman zaɓen wani ɗan takara ko ya nuna alaƙa bayyananna da wata jam’iyyar siyasa.

Ta kuma nemi INEC ta wallafa sunayen jami’an da take shirin nada wa aikin tattara da haɗa sakamakon zaɓe tun kafin ranar zaɓe.

ADC ta shigar da korafi gaban INEC
Sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullaji Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Kotu ta dage shari'ar ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron karar da Nafiu-Bala Gombe ya shigar kan shugabancin jam'iyyar ADC.

Nafiu Bala dai yana neman hana David Mark da shugabannin jam’iyyar ADC gabatar da kansu a matsayin jagororin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng