Matsaya 8 da ‘Yan Takarar Gwamnan ADC a Jihohin Arewa maso Yamma 7 Suka Cinma

Matsaya 8 da ‘Yan Takarar Gwamnan ADC a Jihohin Arewa maso Yamma 7 Suka Cinma

Abuja - Ganin an buga gangar takara a jihohi, masu neman zama gwamnoni a inuwar ADC a Arewa maso yamma sun yi zama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Zaman 'yan takaran Arewa maso yamma na ADC

Zaman da aka yi ya yi sanadiyyar sa hannu a takardar cigaba da aka yi alkawarin za a kawo wa yankin idan an ADC ta zabe be.

'Yan ADC
Masu yi wa ADC takarar gwamna a jihohin Arewa maso yamma Hoto: @DemolaRewaju
Source: Twitter

Demola Rewaju ya fitar da jerin alkawuran da ’yan takaran gwamnan suka dauka, ya yi bayanin a dandalin X a yammacin Laraba.

Kowane ‘dan takaran gwamna ya sa hannu cewa zai cika wadannan alkawura muddin ya yi nasarar shiga ofis daga 2027 zuwa 2031.

Abubakar Malami SAN mai neman zama gwamna a jihar Kebbi ya yi karin haske bayan taron ‘yan takaran na jam’iyyar ADC a jiya.

'Yan takaran ADC a jihohin Arewa maso yamma

Kara karanta wannan

2027: Yan takarar gwamna a Kano da jihohi 6 sun ɗauki matsaya kan dawo da tallafin fetur

Hadimin na Atiku Abubakar, Rewaju ya jero 'yan takaran a shafin X, ya ce idan suka cika wadannan alkawura yankin zai ga cigaban gaske.

  1. Jigawa - Sabo M. Nakudu
  2. Kaduna - Isa Ashiru
  3. Kano - Ibrahim Ali Amin
  4. Katsina - Ahmad Babba Kaita
  5. Kebbi - Abubakar Malami
  6. Sokoto - Manir Muhammad Dan’iya
  7. Zamfara - Bilyaminu Shinkafi

Alkawuran da 'yan takaran suka dauka

1. Goyon bayan Atiku a maido tallafin mai

‘Yan takaran duk sun amince su mara wa Atiku Abubakar baya a alkawarin da ya yi na maido tallafin man fetur idan ya hau mulki a 2027.

Duka masu neman zama gwamnonin a ADC sun yarda cewa janye tallafin da aka yi a 2023 ya jefa mutanen yankin cikin kangin talauci.

2. Sa hanu a takardar alkawari

Kowane ‘dan takara ya amince da takardar alkawuran cigaba da za a kawo wa jihohin Arewa maso yamma bakwai idan aka lashe zabe.

Ban da amincewa da manufofin, ‘yan siyasar sun rattaba hannu da nufin za su kawo wadannan cigaba a jihohin Arewa ta yamma.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta shiga Aso Rock ta dauke ma’aikacin da ya yi aiki da shugabannin kasa 3

3. Alwashin kai albashi akalla N110, 000

Takardar ta kunshi alkawarin kara mafi karancin albashin ma’aikata zuwa akalla N11, 000 a wadannan jihohi idan ADC ta lashe zabe.

Duk da suna goyon bayan maido tallafin mai, sun yi alkawarin daga mafi karancin albashin da ake biyan ma’aikata wanda yanzu N70, 000 ne.

4. Fasaha a yaki da rashin tsaro

Yankin ya dade yana fama da matsalar rashin tsaro, ADC tana kafa gwamnati a jihohi za a shigo da fasaha wajen tabbatar da zaman lafiya.

Za a yi amfani da jirage marasa matuka domin magance matsalar kuma za a kafa cibiya ta musamman da za ta kula da jihohin bakwai.

5. Dokar ta-baci a harkar ilmi

Ana kukan an bar wannan bangare na kasar a baya, saboda haka gwamnatocin ADC za su ayyana dokar ta-baci a sha’anin ilmin zamani.

Za a tabbatar jihohin nan suna samun kason kudinsu na UBEC kuma za a hada karatun almajiranci da tsarin boko na zamanin yau.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun bi bayan ‘dan takaran APC a zaben gwamna, an san makomar Tinubu a Yobe

6. Samar da manyan asibitoci 21

Da APC za ta lashe zaben gwamnoni a jihohin da ake magana, to an dauki alkawarin gina asibitin kwararru a kowace mazaba a yankin.

Wannan yana nufin za a gina manyan asibitoci 21 tare da inganta dakunan shan magani kuma a sama wa jama'a da tsarin inshorar lafiya.

7. Samar da jari ga matasa

Masu burin zama gwamnonin sun sa hannu cewa za su samar da asusu na yankin da nufin rage zaman kashe wando da ake yi.

Wannan tsari zai ba matasa jarin yin kasuwanci kuma za a koyar da su ilmin sana’a da neman kudi domin su iya tsaya da kafafunsu.

8. Kafa kwamitocin kula da tsare-tsaren

Rewaju ya ce an yi alwashin za a samar da kwamiti a karkashin Hon. Abdussamad Dasuki da zai tabbatar da aiwatar da manufofin nan.

Takardar ta ce za a kuma samu wasu kwamitoci karkashin jagorancin kwararru kamar Aminu Bande, Sadiq Abubakar da Salihu Tanko Yakasai.

Kara karanta wannan

Pantami ya ci zaben gwamnan Gombe na gwaji da aka yi a intanet

Jihohi 8 suka dogara da karfinsu

An karanta rahoto cewa kudin shigan da gwamnoni suke samu ba zai biya albashi ba, nauyin ma'aikata ya yi wa jihohi 26 yawa.

Legas, Kaduna da wasu jihohi takwas a Najeriya ne za su iya biyan albashin ma'aikatansu da kudin shiga ba sai da tallafin FAAC ba.

Ba a samu alkaluman kudin da jihohi biyu suka samu da kuma abin da albashi yake ci masu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng