FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasa

FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasa

- Gwamnatin tarayya na kokarin dagewa wurin tallafawa matasa da jari musamman masu kananan sana'o'i don rage rashin aikin yi a Najeriya

- Hidimar shugaban kasa ta musamman, Lauretta Onochie ta sanar da hakan a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter

- Inda tace gwamnatin tarayya ta saki adireshin yanar gizo wadda matasan da basu wuce shekaru 18 zuwa 35 ba zasu bi su samu tallafin

Gwamnatin tarayya na kokarin rage rashin aikin yi a Najeriya, inda ta bayar da adireshin yanar gizo da matasa zasu samu damar samun jari, don tallafawa masu kananan sana'o'i.

Hadimar shugaba Buhari, Laureta Onochie ta sanar da hakan a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba ta kafar sada zumuntar zamani.

Dama ministan matasa da bunkasa wasanni, Sunday Dare, ya sanar da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da naira biliyan 75 don tallafawa matasa.

Yace za'ayi aikinne na tsawon shekaru 3, a kowacce shekara za'ayi amfani da naira biliyan 25, kamar yadda shugaban kasar ya amince.

Onochie tace, "gwamnatin tarayya ta saki adireshin yanar gizo ta shirin NYIF don tallafawa sana'ar matasa masu shekaru 18 zuwa 35."

KU KARANTA: Borno: 'Yan gudun hijira sun koka da rashin samun abinci

FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasa
FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasa. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: Sarkin Kano ya roki lumana da kwanciyar hankali yayin zabe

A wani labari na daban, wasu 'yan gudun hijira dake jihar Borno, sun yi korafi akan rashin samun abinci da kuma zargin sojojin dake tsaresu da cutar da su.

'Yan gudun hijirar guda 37 da basu dade da kubutowa daga hannun 'yan bindiga ba, yanzu haka suna zaune a sansanin gudun hijira dake Dalori a babban birnin jihar, sun yi koke akan tsaka mai wuyar da suka tsinci kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel