Dalilin Barin Gwamnatin Buhari In ji Amaechi da Ya Shekara 7 Yana Minista a APC

Dalilin Barin Gwamnatin Buhari In ji Amaechi da Ya Shekara 7 Yana Minista a APC

  • Rotimi C. Amaechi bai ji dadin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta rika tafiyar da mulki ba
  • Wannan ya sa yayin da yake minista, ya rika janye jiki daga ofishinsa kafin a karshe ya yi murabus
  • Kafin Amaechi ya ajiye aiki da nufin zama ‘dan takarar shugaban kasa, sau daya yake zuwa ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Rotimi Amaechi wanda yake neman zama mataimakin shugaban kasa a ADC a badi ya yi maganar murabus dinsa a 2022.

Rotimi Amaechi ya shafe shekaru kimanin bakwai a matsayin Ministan sufuri a lokacin da Muhammadu Buhari yake mulki.

Rotimi Amaechi
Bukola Saraki, Rotimi Amaechi da marigayi Muhammadu Buhari a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rotimi Amaechi ya tuno da zamansa minista

An yi hira da Rotimi Amaechi a gidan talabijin na AIT, a nan ne aka bijiro da zancen ministan sufuri da ya yi a Gwamnatin tarayya.

Mista Amaechi ya bada labarin yadda ya janye jikinsa daga gwamnatin Buhari da ya zama bai gamsuwa da tafiyar da ake yi.

Kara karanta wannan

Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai

Tsohon gwamna na Rivers ya ce a sakamakon haka ne ya bukaci shugaban kasa ya bar shi ya koma jami’a alhali yana majalisar FEC.

Hakan zai ba shi damar zuwa ofishinsa a Ma’aikatar sufuri sau daya a mako kurum.

Haduwar Rotimi Amaechi da Muhammadu Buhari

Amaechi ya ce ya tunkari marigayi Buhari, yana koka masa cewa gwamnatinsa ba ta iya biya wa ‘yan Najeriya bukatunsu ba.

Yake cewa ya tuna wa tsohon shugaban kasar cewa an zabi APC a 2015 ne saboda an ga irin yadda ya yi mulkin soja a 1983.

Leadership ta rahoto shi yana cewa bayan wannan magana sai kashegari ya sake dawo da zanen komawarsa aiki a jami’a.

Shi kuwa marigayin ya amsa masa cewa yanayin sun sha bam-bam, domin lokacin yana matashi ne kuma a tsarin mulkin soja.

Washegari na koma wajen Mai girma shugaban kasa, na ce ‘zan iya tafiya jami’a?’
Sai ya ce ‘eh’.

- Rotimi C. Amaechi

Amaechi bai zuwa ma'aikata sai ranar Laraba

A aikin da aka ba shi, ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Juma’a kadai yake zuwa ofis, ranar Laraba kuma yana ma’aikata.

Kara karanta wannan

Amaechi ya faɗi sharaɗin yin murabus a gwamnatin Atiku bayan sun yi nasara a 2027

Ya ce:

"Wannan a aikace murabus ne daga gwamnati. Ranar da na ke zuwa aiki Laraba ce kurum."

Hakan ya nuna tun kafin ya rabu da matsayinsa gaba daya domin neman takarar shugaban kasa, ya rage yin aikinsa na minista.

Da ya yi murabus a 2022, Amaechi ya shiga zaben tsaida gwani a jam’iyyar APC, ya zo na biyu bayan Bola Ahmed Tinubu.

Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi da tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rikcin gwamnonin APC da Nyesom Wike

Ana da masaniya cewa Shugaban APC na ƙasa zai sasanta gwamnonin jam’iyyar APC da abokin rigimarsu, Mista Nyesom Wike.

Gwamnonin APC sun ƙalubalanci yunkurin Wike wanda ‘dan jam'iyyar PDP ne wanda yake adawa da su a jihohinsu a zabe mai zuwa.

Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa sabanin ra'ayi abu ne da aka saba da shi a tsarin siyasar dimokuraɗiyya tun fil-azal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng