Pantami Ya Ci Zaben Gwamnan Gombe na Gwaji da aka Yi a Intanet
- Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sami gagarumar nasara a sakamakon gudanar da zabuka biyu daban-daban a yanar gizo a jihar Gombe
- Matakin ya zo ne kwanaki kadan bayan hukumar INEC ta tantance yan takara masu neman kujerar gwamna da yan majalisar jiha na zaben 2027
- Pantami yana daya daga cikin yan takara da ke kan gaba a neman gwamnan jihar ta Gombe tare da Jamilu Isiyaku Gwamna da kuma Bala Bello Tinka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Dan takarar jam'iyyar PDP a Gombe, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya fara nuna rinjaye a fagen siyasar jihar a shirin zaben 2027.
Pantami ya ragargaji sauran 'yan takara a zabukan gwaji biyu daban-daban da aka gudanar a tsakanin masu amfani da kafofin sada zumunta.

Kara karanta wannan
Gwamnan APC ya tona gaskiya, an ji yadda gwamnoni suka amfana da cire tallafin fetur

Source: Facebook
Daily Nigerian ta rahoto cewa a daya daga cikin zabukan yanar gizo da dan jarida Mustapha Musa Kaita ya gudanar a ranar 24 ga Agustan 2026, Pantami ya samu kuri'a 521 daga cikin 676, wanda ya wakilci 77.07%.
Sakamakon zabukan intanet
A wani zaben gwaji na daban da shafin Gombawa ya gudanar don mai da hankali kan abubuwan da ke faruwa a jihar, Pantami ya sake samun rinjaye mai tarin yawa.
The Nation ta wallafa cewa sakamakon zaben ya kasance kamar haka:
"Zuwa karfe 6:32 na safe a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, Isa Ali Pantami ya sami kuri'a 48,968 daga cikin kuri'a 58,358 da aka kada, wanda ke wakiltar kashi 83.91 na jimillar kuri'un."
Sakamakon sauran yan takara
Jamilu Gwamna na APC ne ke biye da shi inda ya sami kuri'a 7,213 (12.36%), yayin da Dr Bala Bello Tinka ya samu kuri'a 2,177 (3.73%).
Wannan adadi yana nufin cewa Pantami ya samu sama da kuri'a hudu cikin kowace kuri’a biyar da aka kada a zaben yanar gizo na Gombawa.

Source: Facebook
Gudunmawar da tsohon ministan ya bayar a harkar mulki da kasancewarsa jigon gwamnatin tarayya a baya na daga cikin abubuwan da ke karfafa wa magoya bayansa gwiwa.
Duk da cewa wadannan zabuka na intanet ba za su taba zama daidai da ainihin zaben zahiri ba, masana na gani sun nuna alkiblar yadda goyon bayan jama'a yake kafin zaben 2027.
Shirin Obi a zaben 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa a shirye yake ya kare kuri'unsa a zaben 2027, ko da hakan na nufin sadakar da rayuwarsa.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a birnin Port Harcourt lokacin da yake amsa tambayoyi a wani taron tattaunawa da masu zabe mai taken "Obi Talks Nigeria".
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kalubalanci sakamakon zaben 2023 da ya gabata, inda ya bayyana cewa an tafka magudi a zaben da ya kai Bola Tinubu ga samun nasara.
Asali: Legit.ng
