Tinubu na da Cikakkiyar Lafiyar da Zai Ci Gaba da Mulkin Najeriya? An Samu Bayani

Tinubu na da Cikakkiyar Lafiyar da Zai Ci Gaba da Mulkin Najeriya? An Samu Bayani

  • Otunba Segun Sowunmi ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da jita-jitar rashin lafiyar Shugaba Bola Tinubu
  • Ya ce Bola Tinubu yana cikin koshin lafiya kuma hankalinsa yana kwance, sannan zai iya ci gaba da jagorantar Najeriya
  • Sowunmi ya bukaci ’yan Najeriya su guji kalaman kiyayya da mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Nigeria - Shugaba kuma wanda ya kafa kungiyar The Alternative Movement, Otunba Segun Sowunmi, ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan lafiyar Shugaba Bola Tinubu.

Sowunmi ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa shugaban kasa yana cikin koshin lafiya kuma hankalinsa yana kwance.

Sowunmi.
Tsohon mai magana da yawun PDP, Segun Sowunmi Hoto: Segun Sowunmi
Source: Twitter

Sowunmi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wani taron tattaunawa da jama’a a Karamar Hukumar Ijebu North ta Jihar Ogun, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ranar yanci: Atiku ya ɗauko batun da yan Najeriya ke buƙata sani kan raba tallafin N75,000

Ya kuma bukaci ’yan Najeriya su guji kalaman kiyayya da kuma abin da ya bayyana a matsayin al’adar murnar munanan abubuwan da ke faruwa a kasar.

Jawabinsa ya zo ne a daidai lokacin da aka sake fara yada rade-radin rashin halartar Tinubu taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA), inda wasu masu ke alakanta hakan da rashin lafiya.

Wasu masusukar gwamnati sun fara tambayar ko yana da lafiyar da zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 har ya ci gaba da mulkin Najeriya.

Bola Tinubu na da cikakkiyar lafiya?

Sowunmi ya yi watsi da rade-radin, yana mai cewa jita-jitar siyasa ce, kuma irin wadannan ikirare-ikiraren an taba yi a baya kan shugaban.

“Shugaban kasa yana cikin koshin lafiya. Shugaban kasa yana cikin hayyacinsa," in ji shi.

Dan siyasar ya bukaci ’yan Najeriya kada su bari sabanin siyasa ya koma abin da ya kira “ci gaba da kyamar kai”, yana mai cewa wasu mutane sun fi nuna sha’awar labarai munana fiye da masu dadi.

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

Sowunmi ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin dabi’ar wasu ’yan Najeriya da abokan hamayyar siyasa na mayar da hankali fiye da kima kan munanan abubuwan da ke faruwa.

Sowunmi ya soki ’yan adawa

Sowunmi ya kuma soki wasu ’yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun adawa, yana mai cewa sun gaza amincewa da ci gaban da ake samu yayin da suka maida hankali kan kalubalen kasar.

Segun Sowunmi.
Tsohon jigon jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: Segun Sowunmi
Source: Facebook
"Ba za su taba murna idan wani abu mai kyau ya faru a Najeriya ba. Da zarar sun ji akwai wata karamar matsala, sai su fara murna," in ji shi.

Sowunmi ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa Tinubu zai lashe Jihar Ogun a zaben shugaban kasa na 2027, yayin da ya bukaci mazauna jihar su fito da yawa domin kada kuri’a, cewar rahoton Leadership.

Fadar shugaban kasa ta yi magana

Kun ji cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya duk da rashin ganinsa a Abuja da taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Fadar ta ce a wannan zamani na fasahar sadarwa, ba lallai ne Shugaban Ƙasa ya kasance a Abuja a zahiri ba kafin ya iya gudanar da ayyukan da aka zaɓe shi domin yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262