Menk: Babban Malamin Musulunci a Duniya Ya Ba Rahama Sadau Shawara
- Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta nuna damuwa kan yadda wasu kamfanonin tafiye-tafiye ke ɗaukar hotuna da bidiyon masu zuwa Umrah domin tallata ayyukansu
- Rahama ta ce tana sha’awar zuwa Umrah cikin jama'a, amma yadda ake mayar da hankali kan ɗaukar hotuna da bidiyoyin mahajjata na sanyaya mata gwiwa
- Fitaccen malamin addinin Musulunci, Mufti Menk, ya mayar da martani kan koken Rahama, inda ya ba ta shawarar wani kamfanin da ya ce zai ba ta damar gudanar da Umrah cikin sirri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta koka kan salon wasu kamfanonin tsara tafiye-tafiye na ɗaukar hotuna da bidiyon masu gudanar da ibadar Umrah domin tallata ayyukansu.
Rahama ta bayyana damuwarta ne a wani saƙo, inda ta ce tana son ta samu damar zuwa Umrah cikin jama'a ba tare da shiga cikin ɗaukar hotuna da bidiyon talla ba.

Source: Facebook
Korafin da Rahama Sadau ta yi
A sakon da ta wallafa a Facebook, Jarumar ta ce salon wasu kamfanonin na ƙirƙirar abun da za a wallafa a kafafen sada zumunta yayin tafiyar Umrah na matuƙar sanyaya mata gwiwa.
Ta ce mutane da dama suna kallon tafiyar Umrah a matsayin wata ibada mai tsarki, inda wasu ma ba sa son a wallafa hotunansu sai bayan sun dawo daga ƙasa mai tsarki.
Rahama ta yi tambaya ko akwai kamfanonin tafiye-tafiye da ke shirya Umrah ga jama'a ba tare da ɗaukar bidiyon masu ibadar domin wallafa su a kafafen sada zumunta ba.
Mufti Menk ya ba ta shawara
Martanin Rahama ya jawo hankalin Mufti Menk, wanda ya ba ta shawarar wani kamfanin tafiye-tafiye da ya ce zai iya shirya mata tafiyar Umrah cikin sirri.
Mufti Menk ya ce Rahama za ta iya duba kamfanin DST World Travel, inda ta saye tikitin tafiyar Umrah ta kashin kanta domin samun abin da take nema.
Ya kuma ce idan ta zaɓi tafiya cikin jama'a, za ta iya sanar da masu shirya tafiyar tun da wuri cewa ba ta son a saka ta cikin hotuna ko bidiyon da za a ɗauka.

Source: Instagram
Za a hukunta mawakiyar Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kotun ɗaukaka ƙara a Iran ta tabbatar da hukuncin bulala 74 da aka yanke wa fitacciyar mawaƙiya Parastoo Ahmadi bayan ta yi waka ba tare da sanya hijabi na tilas ba.
An gurfanar da Ahmadi mai shekara 29 bayan wani bidiyon waƙar da ta yi sanye da riga mara hannaye ya bazu sosai a watan Disamban 2024, inda hukumomin shari’ar Iran suka ce wasan ya saɓa wa dokokin ƙasa da al’adunta.
A watan Yuni, wata kotun laifuka da ke Qom ta rahoto cewa ta samu Ahmadi da wasu mutum takwas daga cikin ƙungiyar mawaƙanta da masu shirya waƙar da laifuka da suka haɗa da ɓata tarbiyyar jama’a.
Asali: Legit.ng

