2027: Yan Takarar Gwamna a Kano da Jihohin 6 Sun Dauki Matsaya kan Dawo da Tallafin Fetur
- Yan takarar gwamnan na jam'iyyar ADC a jihohin Arewa maso Yamma bakwai sun bukaci Bola Tinubu ya dawo da tallafin fetur
- Sun bayyana cewamatakin cire tallafin ya kara tsananta matsalar tsadar rayuwa da talauci a yankin Arewa da ma kasa baki daya
- Yan takarar sun yi alkawarin amfani da jirage marasa matuka da fasaha wajen yaki da rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yan takarar gwamnan jam'iyyar ADC) a jihohi bakwai na yankin Arewa maso Yamma sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye matakin cire tallafin fetur.
Yan takarar sun ce cire tallafin fetur ya kara tsananta matsalar tsadar rayuwa da talauci da al'ummar yankin ke fama da su.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yan takarar daga jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Jigawa ne suka gabatar da wannan bukata ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan
2027: An samu babbar matsala a yunkurin fitar da ɗan Takara 1 tsakanin Atiku, Peter Obi da Makinde
Hakan ya faru ne yayin da suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai suna Northwest ADC Governorship Candidates' Compact 2027-2031.
Malami ya gabatar da takardar yarjejeniya
Tsohon Ministan Shari'a kuma Antoni Janar, Malam Abubakar Malami, SAN, wanda shi ne dan takarar gwamnan ADC a jihar Kebbi, ya gabatar da takardar yarjejeniyar.
Yan takarar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga alkawarin dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin fetur idan aka zabe shi.
Malami ya ce dawo da tallafin na daga cikin matakan gaggawa da ya kamata a dauka domin rage matsanancin halin kunci da al'ummar yankin ke ciki.
Ya ce:
"Mu, yan takarar gwamnan ADC na jihohi bakwai na Arewa maso Yamma, muna bayyana cikakken goyon bayanmu ga alkawarin da dan takarar shugaban kasarmu, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi na dawo da tallafin fetur.
"Wannan na daga cikin matakan gaggawa da za a dauka domin dakatar da ci gaba da jefa al'ummarmu cikin matsanancin talauci."
Illar da cire tallafin ta jawo a Najeriya
Yan takarar sun yi zargin cewa cire tallafin fetur ya kara tsananta wahalhalun da iyalai ke fuskanta a yankin.
Sun ce fa'idodin da ake tsammanin samu daga cire tallafin ba su bayyana ta hanyar inganta rayuwar talakawan Najeriya ba.
Yan takarar sun yi zargin cewa duk da makudan kudaden da jihohin ke samu daga Asusun Tarayya, ba a ga irin ci gaban da ya kamata a fannonin samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, wadatar abinci da tsaro ba.

Source: Facebook
Sun dauki alkawari kan rashin tsaro
Dangane da matsalar tsaro, yan takarar sun ce mutane sama da 16,000 sun rasa rayukansu sakamakon rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Sun kuma yi ikirarin cewa an samu sama da hare-haren sace mutane 1,583 tun daga watan Janairun 2023.
Domin magance matsalar rashin tsaro, yan takarar sun yi alkawarin amfani da jirage marasa matuka wajen sanya ido a fadin yankin, sannan za su kafa Cibiyar Hadin Gwiwar Tsaro ta Yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya ware gwamnonin Arewa, ya fadi matsalan da za su fuskanta a zaben 2027
Haka kuma, sun yi alkawarin samar da tsarin sanya ido da amsa kiran gaggawa ta amfani da fasaha a kowace daga cikin mazabun sanatoci 21 na yankin.
Trump ya goyi bayan shirin Atiku
Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce Shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan shirinsa na dawo da tallafin man fetur.
Atiku ya ce manufarsa za ta mayar da kuɗi cikin aljihun ‘yan Najeriya ta hanyar tallafa wa samar da man fetur da tace shi a cikin ƙasa.
Asali: Legit.ng
