Atiku Abubakar Ya Jero Masu Amfana da Cire Tallafin Man Fetur da Tinubu Ya Yi
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi ya kawo tsadar rayuwa, sufuri da kayan abinci
- Idan ya samu mulki, tsohon mataimakin shugaban kasar zai sa gwamnati ta koma kan tsarin tallafi domin rage tsadar rayuwa
- Ya ce 'yan kasuwa na tafiya saboda kwastomomi ba su da kudin sayen kaya, yayin da tallafi ke zuwa ga abokan gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Aitku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Tinbu da jefa mutane a cikin kangin talauci.
‘Dan takarar shugaban kasar yana ganin gwamnati ta fito da tsare-tsaren tattalin arziki da suka tsiyata jama’a kuma suka kashe kasuwanci.

Source: Facebook
Atku Abubakar ya ce an jefa mutane a talauci
Leadership ta rahoto Atiku Abubakar yana cewa an bar aljihun jama’a babu komai kuma an jawo kudi bai da daraja ban da tsadar kaya.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki zafi da ya ga rahoton yadda aka raba tallafin N25,000 ga yan Najeriya
An samu maganar ‘dan takarar ne a a wani jawabi da hadiminsa, Phrank Shaibu ya fitar, yana sukar wasu alkaluman da ake fitarwa.
‘Dan adawar yake cewa ba za a labe da alkaluman tattalin arziki da suke nuna ana samun cigaba ba, alhali a zahiri jama’a suna kuka.
Sakamakon cire tallafin man fetur
Atiku yake cewa da Tinubu ya janye tallafin fetur, an samu tashin farashin mai, kudin zirga-zirga da kuma tsadar kayan abinci a kasuwa.
Jawabin ya ce matsayar ‘yan kungiyar CORAN da yunkurin Donald Trump a harkar man Najeriya ya nuna raunin manufar Bola Tinubu.
‘Yan kasuwa da ke karkashin CORAN suna goyon bayan a inganta harkar tace mai a gida.
Atiku: Shugaba Tinubu ya jawo tsadar rayuwa
Mista Phrank Shaibu ya ce Tinubu bai da uzurin cewa haka ya gaji tattalin arziki, domin shi ya haifar da tsadar rayuwan da ake ciki.

Kara karanta wannan
"Ka yi yadda na yi," Atiku ya sake kinkimo magana mai girma kan bayanan Tinubu na Amurka
“Ya karbe saukin da mutane suke samu, ya jawo mai, abinci, kudin mota da dawainiyar rayuw suka kara tsada
Kuma yau yana so ‘yan Najeriya su yaba wa alkaluman tattalin arziki alhali babu komai a cikin aljihunsu.
- Atiku Abubakar
Su wane ne ke cin moriyar cire tallafi?
Jawabin ya ce kamfanoni na fama da bashin kudin wuta saboda karin da aka yi a lokacin da yake zargin na kusa da Tinubu da shanawa.
Yake cewa mutanen shugaban kasar da kuma manyan masu harkar mai ne ke morewa a yau amma sauran ‘yan kasuwa suna rasa abin yi.
Ya ce:
"Kamfanoni ba su samun ciniki, mutane kuma ba su iya sayen kaya saboda tsarin tattalin arzikin Tinubu ya zuke karfin aljihunsu."

Source: Facebook
Atiku ya bar 'yan Najeriya da zabi
‘Dan takaran na ADC ya ce al’umma sun ga irin salon mulkin Tinubu a rayuwarsu, yanzu ba su bukatar kara hakuri illa neman agaji.
Ya ce yanzu zabi ya rage wa mai shiga rijiya, a cigaba da tafiya a haka ko kuma su zabi wanda zai azurta su kuma ya kawo ayyukan yi.

Kara karanta wannan
Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba
Man fetur na iya kara tsada a Najeriya
An samu labari cewa a lokacin da ake kukan lita ta wuce N1300, yakin Amurka-Iran zai iya jawo karin kudin fetur a gidajen man da ke Najeriya.
Rikicin Amurka da Iran ya sake tsananta, wanda hakan ya sa farashin man fetur na Brent tashi sama da $90 a cikin watan Satumban nan na 2026.
A kasuwar duniya, man Najeriya ya tashi da akalla 4.6%, hakan yana nufin kowace ganga na neman kai $95 saboda rikici da ake ta yi da Iran.
Asali: Legit.ng