Jihohi 26 Sun Dogara da Tarayya har Ta Kai ba Za Su Iya Biyan Albashi da Kansu ba
- Jihohi takwas kacal daga cikin 34 ne kudin shigarsu na cikin gida a shekara suka fi yawan albashin ma'aikatansu
- Binciken BudgIT ya nuna cewa rabon kudin FAAC sun karu zuwa 232% bayan cire tallafin man fetur da aka yi a 2023
- Masana tsimi da tanadi sun bukaci gwamnoni su rage batar da kudi a kan ma'aikata, su gano sababbin hanyoyin samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jihohi akalla 26 ne suka dogara da FAAC, ba su samun kudin shiga sosai da za su isa su ji da dawainiyar albashi a shekarar 2025.
Jihohin Lagos, Enugu, Ogun, Delta, Kaduna, Kwara, Abia da Anambra ne kawai kudin da suke samu (IGR) zai isa su biya bukatun ma'aikata.

Source: Facebook
Jihohi 8 za su iya biyan albashi da kansu
Punch ta yi nazarin kudin da gwamnoni 34 suke samu, ta gano takwas dinnan ne kawai za su iya tsaya wa da kudin shiga (IGR) a shekara.
Ko ba su samu sisin kobo daga kason FAAC ba, gwamnatocin Legas, Kaduna da sauran jihohin nan za su iya biyan ma'aikata hakkokinsu.
Akwa Ibom da Rivers ba su cikin jihohin da aka yi nazari saboda ba a samu bayanan kudin da suka samu da abin da suka kashe a 2025 ba.
Albashin jihohi 26 ya dogara kan kason FAAC
Ragowar jihohin kasar 26 sun tatso N1.16tr a shekarar bara, amma sun kashe N1.91tr wajen biiyan ma'aikata, sun bar gibin fiye da N740bn.
Jihohin nan sun dogara da abin da ake raba wa gwamnatoci a FAAC bayan an tattaro duk kudin da Najeriya ta samu a kowane wata.
Binciken BudgIT ya nuna abin da ake raba wa a FAAC ya karu daga N3.4tr a 2022 zuwa N11.38tr a 2025, an samu karin 232% kenan.
Kudin shigar gwamnati ya karu sosai daga N1.57tr zuwa N4.15tr a tsawon wannan lokaci. Karin 165% bayan an cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan
Kano da wasu jihohi 7 da cutar 'Diphtheria' ta fi kama mutane, NCDC ta gano matsalar
Duk da karin kudin shiga, gwamnatoci sun kara dogara sosai da FAAC a shekarar bara. Wannan ya nuna raunin da jihohi suke da su.
Jihohin da suka fi kowane dogara da FAAC a 2025
Oyo da ta samu N120bn da kan ta a bara, ta kashe N170bn, watau an bar gibi har na N67bn.
Yobe na cikin jihohin da lamarinsu ya fi muni domin N15bn kadai ta tatso da kan ta, amma biyan albashi ya ci mata fiye da N76bn.
Taraba ta samu N17.8bn amma ta kashe N55bn, haka lamarin yake a Sokoto da ta kashe N58bn bayan ta iya samun N20.5bn.
Adamawa da ta batar da N65bn ta samo N24bn. Jigawa da Benuwai sun kashe N92bn da N73bn amma N35bn da N29bn suka samu.
N36bn ne abin da Kogi ta samu daga IGR, amma ta kashe N89bn, sai jihar Kebbi da ta iya kashe N44bn duk da N18bn ta iya tatsowa.

Source: Facebook
Ragowar jihohin da IGR bai biyan albashi
Rahoton ya ce lamarin duk daya ne a Bauchi, Bayelsa, Borno, Cross River, Ebonyi, Edo, Ekiti, Gombe, Imo, Kano sai kuma Katsina.

Kara karanta wannan
"Ka yi yadda na yi," Atiku ya sake kinkimo magana mai girma kan bayanan Tinubu na Amurka
Haka zalika Nasarawa, Niger, Ondo, Osun, Oyo, Plateau da Zamfara ba su iya nemo wa kansu kudin da suke bukatar kashewa a albashi.
Kashim Shettima bai son facaka da kudi
An ji labari cewa Mataimakin Shugaban Kasa bai bukatar a kawo masa kyauta ko wasu kayan duniya saboda taya shi murnar ya cika shekara 60.
Kashim Shettima ya bukaci masoyansa da kada su kashe kudi wajen taya shi murnar cika shekaru 60, maimakon haka su yi masa da kasa addu'a.
Mataimakin Shugaban Najeriyar ya ba masoya shawarar su batar da kudin wajen taimaka wa marasa karfi, ya ce yin hakan ya fi muhimmanci.
Asali: Legit.ng
