Ciwon Zuciya Ya Yi Kamari: Gwamnatin Tinubu Ta Nemo Dabarun Yaki da Cutar

Ciwon Zuciya Ya Yi Kamari: Gwamnatin Tinubu Ta Nemo Dabarun Yaki da Cutar

  • Gwamnatin tarayya ta yi kira da a ƙara ƙoƙarin hana cututtukan zuciya, gano su da wuri da kuma inganta damar samun magani
  • Ta ce sahihin bayanai kan lafiyar zuciya na tana kira ga gwamnati da kwararru su ƙara wayar da jama’a
  • Kungiyar Heart Recovery Foundation ta ce ayyukanta sun haɗa da wayar da kai, gwaje-gwaje da tallafa wa marasa galihu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya yi kira da a ƙara ɗaukar matakan hana cututtukan zuciya da jijiyoyin jini.

Ya kuma buƙaci a inganta gano cututtukan da wuri tare da faɗaɗa damar samun magani, yana mai jaddada muhimmancin sahihin bayanan jama’a wajen ceton rayuka.

Gwamnatin Tinubu ta yi gargadi kan cutar zuciya a Najeriya
Ministan yada labarai, Mohammed Idris da wasu marasa lafiya yayin wayar da kai kan cututtukan zuciya. Hoto: Federal Ministry of Information.
Source: Facebook

Idris ya yi wannan kiran ne ranar Talata a Abuja, cikin saƙon da ya aike ta hannun Darakta-Janar na FRCN, Dr Mohammed Bulama da aka wallafa a shafin ma'aikatar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Wike ya fadi abin da zai sa ya yi murabus a gwamnatin Tinubu

Cututtukan zuciya: Gwamnatin Tinubu ta ba da shawarwari

An gabatar da saƙon ne a wajen bikin Ranar Zuciya ta Duniya ta 2026 da kuma bikin bayar da lambar yabo ta musamman kan ayyukan jinƙai.

Kungiyar Heart Recovery Foundation ce ta shirya taron, wanda ya samu halartar kwararrun likitoci, masu fama da cututtukan zuciya da waɗanda suka tsira daga cutar.

Ministan ya ce taron ya tunatar da jama’a cewa akwai mutane da iyalai a bayan kowace ƙididdiga da ake samu kan cututtukan zuciya.

Ya yaba wa Heart Recovery Foundation saboda mayar da damuwa kan cututtukan zuciya zuwa ayyukan zahiri da ke taimaka wa jama’a.

Ministan ya ce ayyukan ƙungiyar sun haɗa da wayar da kai kan lafiya, gwajin cututtukan zuciya, shawarwarin likitoci da sauraron labaran waɗanda suka tsira.

Haka kuma ƙungiyar tana tallafa wa marasa galihu masu fama da cututtukan zuciya domin su samu damar yin magani.

An bukaci hadin kai kan yaki da cututtukan zuciya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto; Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Original

Cututtukan zuciya: An bukaci wayar da kan jama'a

Kara karanta wannan

Bayan matsalolin da aka samu, shugaban hukumar bogi Ta PFIPC ya bayyana a gaban kotu

Da yake magana kan muhimmancin bayanai wajen kariya daga cututtuka, Mohammed Idris ya ce jama’a na buƙatar sahihin bayani mai sauƙin fahimta kan lafiyar jiki.

Ya ce:

“Jama’a na buƙatar sahihin bayani mai sauƙin samu da fahimta kan rayuwa mai lafiya, alamomin cuta da abubuwa masu haɗari."

Ya ce ya kamata jama’a su kuma san lokacin da ya dace su nemi kulawar likita domin samun taimako cikin gaggawa.

Ministan ya jaddada cewa gwamnati, kwararrun lafiya, ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai dole su ci gaba da aiki tare.

Tinubu ya shirya seta Najeriya

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana bangaren da zai mayar da hankali domin sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya.

Tinubu ya ce gwamnati za ta rage kuɗin samar da kayayyaki da sufuri, tare da bunƙasa noma, masana’antu da ayyukan yi.

Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun jawo wahala, amma gwamnati za ta ci gaba da su tare da ƙarfafa tallafin marasa galihu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.