Sarakuna Sun Bi Bayan ‘Dan Takaran APC a Zaben Gwamna, An San Makomar Tinubu a Yobe
- Tawagar Baba Malam Wali ta ziyarci masarautu 13 daga cikin 14 da ke Yobe domin neman albarka da goyon baya
- Sarakunan gargajiya daban-daban suna goyon bayan jam’iyyar da ke kan mulki ta cigaba da rike madafun iko a 2027
- Shugaban jam'iyyar APC na Jihar Yobe, Muhammad Gadaka, ya tabbatar da cewa jama’a za su zabi Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Yobe - Sarakunan gargajiya a fadin jihar Yobe sun nuna goyon bayansu ga takarar Alhaji Baba Malam Wali a inuwar jam'iyyar APC.
Ba a nan kadai suka tsaya ba, masu kasar suna tare da Bola Ahmed Tinubu, suna so ya zarce a zaben shugaban kasa na 2027.

Source: Facebook
Baba Malam Wali ya samu goyon bayan sarakunan Yobe
Baba Malam Wali ya yi wannan bayani lokacin da yake zantawa da sarakunan da ake da su a jihar a cewar rahoto daga jaridar Leadership.
‘Dan takaran gwamnan ya kai wa sarakunan gargajiya ziyara, ya ce ya yi wannan ne domin ya gode saboda nuna goyon bayansu.
Baya ga godiya, ‘dan siyasar ya kuma nemi wadannan sarakuna su taimaka masa da addu’o’i domin ganin ya yi nasara a zabe mai zuwa.
Baba Malam Wali ya ce zuwa yanzu sun ziyarci fadar sarakuna 13 daga cikin 14 da ake da su a Yobe domin a sa wa takararsa albarka.
Nan ba da jimawa kuma tsohon sakataren gwamnatin na jihar Yobe yana sa ran za su je wajen ragowar sarkin da ba su ziyarce shi ba.
Sarakuna sun tofawa takarar Bola Tinubu albarka
Masu mulkin gargajiyan sun nuna suna tare da takararsa a jam’iyyar APC har ma wasu suka ba shi sarauta lokacin da ya je fadarsu.
A game da Bola Tinubu da yake neman tazarce kuwa, Wali ya bayyana cewa tafiyar shugaban kasar tana ganin haske a jihar Yobe.
Yake cewa babu inda suka fuskanci kalubale wajen tallata tazarcen Mai girma Tinubu a jihar Yobe.
“Mun riga mun fada wa kowa cewa Mai girma shugaban kasa ya yi kokari, kuma mun yi imani za a sake zaben shi a 2027.
- Baba Malam Wali
Shugaban APC yana ganin nasara a Yobe
‘Dan takaran ya kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan jam’iyyar da magoya baya da kungiyoyi su hada kansu a jihar.
Shugaban APC na reshen Yobe, Muhammad Gadaka, ya ce jam’iyyarsu tana neman albarkar sarakunan gargajiya a takarar badi.
Alhaji Muhammad Gadaka ya ce sarakuna suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da hadin kai da kuma ganin an yi zabe lafiya.
'Dan siyasar ya ke cewa yada aka zabi Baba Malam Wali, haka jama’a za su zabi Bola Tinubu.
Baba Malam Wali da ya ziyarci fadar wani sarki
‘Wannan ba damukaradiyya ba ce’ - Duke
Ana da labari ‘dan takarar shugaban kasa a PRP, Donald Duke ya ce gara mulkin soja a kan gwamnatin da ake gani a yau a Najeriya.
Tsohon gwamnan na jihar Kuros Riba, ya ce 'yan Najeriya sun fi jin daɗin rayuwa a shekarar 1999 fiye da yanzu. da ake mulki na farar hula.
Daga 1979 zuwa 1983 da Shehu Shagari ya yi mulki, Donald Duke yana ganin cewa ba a samu wani cigaba ta fuskar tatalin arzikin kasa ba.
Asali: Legit.ng


