Peter Obi Ya Bayyana Halin Tinubu da ba Zai Dauka ba idan Ya Zama Shugaban Kasa
- Peter Obi ya ce ba zai yi hutunsa a ƙasashen waje ba idan ya zama shugaban Najeriya, inda zai riƙa ziyartar jihohin ƙasar
- Obi ya ce zai jagoranci Najeriya bisa gaskiya, rikon amana da adalci, tare da mayar da hankali kan tsaro, ilimi da tattalin arziki
- Ɗan takarar NDC ya ce Najeriya na fuskantar matsalolin talauci, rashin tsaro, yunwa da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya yi magana kan inda zai rika yin hutu idan ya samu mulkin Najeriya.
Peter Obi ya ce ba zai riƙa yin hutunsa a ƙasashen waje ba idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Obi ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya yi ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2026 domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
Dan takarar shugaban kasar ya ce zai riƙa yin hutunsa a sassan ƙasar idan aka ba shi damar jagoranci.
“Zan riƙa yin hutu a jihohin Najeriya”
Obi ya ce a cikin shekaru huɗu da zai yi a matsayin shugaban ƙasa, zai riƙa ziyartar jihohin Najeriya a lokacin hutunsa domin ya ƙara fahimtar ƙasar da kuma sauraron matsalolin jama’a.
“Tsawon shekaru huɗu da zan yi a matsayin shugaban wannan babbar ƙasa, ba zan yi hutuna a wajen Najeriya ba."
“Zan yi hutuna a Jihar Zamfara, Jihar Borno, Jihar Kwara, Jihar Ebonyi, Jihar Edo, Jihar Ekiti da sauran jihohin Najeriya."
"Ina son ci gaba da ganin Najeriya. Ina son sanin Najeriya. Ina son samun lokaci tare da ’yan Najeriya, sauraron su, fahimtar ƙalubalen da suke fuskanta da kuma yin bikin juriyarsu.” In ji shi.
Maganar Obi na zuwa bayan sukar tafiye-tafiyen Tinubu
Maganar Obi ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun suka kan tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙasashen waje, ciki har da lokacin hutu.
Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya ranar Talata bayan shafe kusan wata guda a nahiyar Turai.
Obi ya yi alkawarin gina Najeriya mai tsaro
Obi ya ce idan aka ba shi damar jagorantar Najeriya, zai yi aiki wajen gina ƙasa mai tsaro, haɗin kai da kuma ƙarfin tattalin arziki, TheCable ta kawo labarin.
Ya ce zai gudanar da gwamnati bisa ƙwarewa, rikon amana da adalci. A cewarsa, burinsa shi ne gina Najeriya inda babu wani yaro da za a hana ilimi saboda matsanancin talauci ko rashin tsaro.
Ya kuma ce zai yi aiki wajen tabbatar da cewa mata ba sa mutuwa saboda rashin samun kulawar lafiya, manoma za su koma gonakinsu cikin tsaro, yayin da matasa za su samu damar yin aiki da bunƙasa rayuwarsu.
Dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa kuɗaɗen gwamnati za a yi amfani da su ne domin amfanin jama’a.

Source: Facebook
Obi ya ce zai dawo da tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya sake shawara kan dawo da tallafin man fetur.
Peter Obi ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa gwamnatinsa za ta fara yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.
Asali: Legit.ng
