Mutuwa Ta Shiga Aso Rock Ta Dauke Ma’aikacin da Ya Yi Aiki da Shugabannin Kasa 3
- Peter Onwubuariri ya rasu a birnin Kano yana dan shekara 48 bayan ya yi fama da jinya ta tsawon lokaci
- Ya yi aikin jarida da gaskiya tare da yi wa shugabannin kasa guda uku hidima a fadar fadar shugaban kasa
- Shugaba Bola Tinubu ya mika ta'aziyyarsa ga iyalansa, yana mai addu'ar Ubangiji ya ba su hakurin jure rashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Peter Onwubuariri wanda babban jami’i ne a fadar Aso Rock Villa ya yi ban kwana da duniya a ranar Litinin.
Mataimakin darektan na harkokin sadarwa a fadar shugaban kasa ya cika ne a asibiti bayan ya yi ta fama da rashin lafiya.

Source: Facebook
'Dan jarida a Aso Rock ya mutu
Rahoton Leadership ya ce kafin ya mutu, Peter Onwubuariri kwararre kuma tsohon ‘dan jarida ne da yake aiki da hukumar NAN.
Ma’aikacin na hukumar dillacin labarai na kasa ya bar duniya yana shekara 48 in ji matarsa, Catherine Ezinna Onwubuariri.
An ce marigayin ya mutu ne a wani asibitin cutar daji da yake Kano, ya yi sallama da duniya ranar 7 ga watan Satumba 2026.
Gwamnatin jihar Kano ta ke dawainiyarsa da yake jinya. Yanzu haka an karbi gawarsa daga asibitin Malam Aminu Kano.
Za a birne Peter Onwubuariri a Imo
Punch ta ce za a wuce da gawar zuwa garin Owerri a jihar Imo inda a nan ne za a birne shi.
Mataimakin darekta na harkokin yada labarai da hulda da jama’a a fadar shugaban kasa, Oche Egwa, ya karbi gawar ta shi.
An damka wa Egwa gawar a madadin Bayo Onanuga wanda shi ne Mai taimakon shugaban kasa wajen yada labarai da dabaru.
Sakon ta'aziyyar shugaban kasa Bola Tinubu
A wani jawabi da Mista Onanuga ya fitar da yammacin ranar Talata ya ce shugaban kasa ya yi takaicin samun labarin rasuwar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mutuwar ‘dan jaridar kuma ma’aikacin a matsayin babban rashi ga fadar shugaban Najeriya.
Ya kuma ce rashin ya shafi hukumar dillacin labarai na kasa, ‘yan jarida da fadin Najeriya.
Daga harkokin kasa da na ketare, shugaba Tinubu ya ce marigayin ya rika kawo rahotanni har zuwa labaran siyasa da tattali.

Source: Facebook
Tarihin da marigayi ya bari a aikin jarida
A shekarar 2014 aka turo Onwubuariri zuwa fadar shugaban kasa bayan ya kasance wakilin NAN a nahiyar Arewacin Amurka.
Da yake raye, ya yi aiki da shugabannin kasa uku a jere; Dr. Goodluck Jonathan, Muhammadu Buhari sai kuma Bola Tinubu.
Lawal Daura ya tona maciya amanar Buhari
Tinubu ya yaba da yadda Onwubuariri ya sadaukar da kan shi wajen aikin jarida aka kuma yi wa iyali da danginsa ta’aziyyar rashin.
An ji labari Lawal Daura ya bayyana wadanda suka ci amanar Marigayi shugaba Buhari lokacin da yake mulki a fadar Aso Rock.
Lawal Daura ya fito da kuskuren da Muhammadu Buhari ya yi da yake mulki da kuma wadanda suka ci amanarsa bayan ba su mukamai.
Tsohon shugaban na hukumar DSS ya zargi gwamnatin da ta wuce da bada mukamai ga wadanda ba su cancanci kujerunsu ba.
Asali: Legit.ng
