Yadda Batun Maido Tallafin Mai Ya Zafafa Adawa tsakanin Tinubu da Atiku

Yadda Batun Maido Tallafin Mai Ya Zafafa Adawa tsakanin Tinubu da Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kalubalanci gwamnatin Bola Tinubu game da cire tallafin man fetur da batun wutar lantarki, lamarin da ya zafafa adawa a tsakaninsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar (ADC), Atiku Abubakar, ya kalubalanci Bola Ahmed Tinubu ya bincike shi tare da gurfanar da shi a kotu idan yana da hujjar cewa ya aikata ba daidai ba.

Atiku ya jefa kalubalen ne yayin da yake mayar da martani kan zarge-zargen da suka sake tasowa kan yadda aka kashe kudi masu yawa kan wutar lantarki da tallafin mai.

Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Shugaba Bola Tnubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Paul Ibe
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku yadda adawa ta zama sabuwa a Najeriya, musamman tsakanin Bola Tinubu da Atiku kan wutar lantarki da cire tallafin mai.

Kara karanta wannan

'Na san ainihin shekarun shugaba Tinubu': Atiku ya ce yana da hujjoji masu ƙarfi

Ina kudin tallafin man fetur?

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin Tinubu ta bayyana yadda aka yi amfani da kudin da aka ce gwamnati ta tanada bayan cire tallafin man fetur.

Ya ce bai kamata sake dawo da tsofaffin zarge-zarge ya hana 'yan Najeriya neman bayani kan yadda ake tafiyar da kudin jama'a ba.

Atiku ya yi tambaya da cewa:

"Kun cire tallafi. Kun karbi kudin da aka ce an ceta. To ina kudin suke?"
Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi na gaisawa da Atiku Abubakar. Hoto: Paul O Ibe
Source: Facebook

Atiku ya ce cire tallafin mai ya jefa 'yan Najeriya cikin tsadar rayuwa, sakamakon tashin farashin man fetur, sufuri da sauran kayayyakin masarufi.

Maganar fadar shugaban kasa

Mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce Atiku ya sauya matsaya sau da dama kan batun ko zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi shugaban kasa.

A cewar Onanuga, daya daga cikin masu magana da yawun Atiku ya fara cewa tsohon mataimakin shugaban kasar zai dawo da tallafin sannan daga baya a cire shi.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa yake son dawo da tallafin fetur

Hadimin shugaba Bola Tinubu
Bayo Onanuga da ke magana da yawun Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya ce wani daga cikin hadiman Atiku ya ce bayanin ba ya wakiltar ainihin matsayar dan takarar na ADC, kafin daga baya Atiku ya ce zai dawo da abin da ya kira tallafi na musamman da zai shafi wasu bangarori.

Onanuga ya ce wannan sabani ya nuna cewa akwai bukatar Atiku ya bayyana dalla-dalla yadda tsarin tallafin da yake shirin aiwatarwa zai kasance.

"Ba batun amfani da kalmomi kawai ba ne. Wannan babban sabani ne a kan manufar tattalin arziki,"

In ji Onanuga.

APC ta ce Atiku Abubakar ya je kotu

Yayin da ake cigaba da musayar kalamai masu zafi tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu ne dan takarar ADC ya ce yana fafatawa da barayi ne a 2027.

A wani bangare kuma, jam'iyyar APC ta kalubalanci Atiku da ya je kotu idan yana da hujjar tabbatar da ikirarin da ya yi cewa wasu "barayi" ne ke da alhakin matsalolin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ban da Atiku,' Dan takara 1 da ya bugu kirji kan shi kadai zai iya maido tallafin mai

Sai dai jam'iyyar APC ta ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasar ya gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi maimakon yin kalaman siyasa.

Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya
Shugaban APC, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

NANS ta taya Bola Tinubu yaki

Kungiyar daliban Najeriya ta NANS ita ma ta soki shawarar Atiku ta dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027.

Shugaban kungiyar, Akinteye Babatunde, ya ce dawo da tsohon tsarin tallafin mai ba tare da yin sauye-sauye masu zurfi ba zai iya sake haifar da matsalolin da suka sa tsarin ya zama nauyi ga tattalin arzikin Najeriya.

Ana zuba fetur a gidan mai
Mutane na sayen fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa Atiku ya ci gaba da cewa 'yan Najeriya na bukatar man fetur mai saukin farashi domin rage tsadar sufuri da rayuwa.

Atiku ya nemi a gurfanar da shi

Hadimin Atiku, Phrank Shaibu, ya Atiku ya ce bai kamata gwamnati ta ci gaba da yada zarge-zarge ba tare da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu ba.

The Cable ta wallafa cewa ya ce tun bayan barinsa gwamnati a shekarar 2007, gwamnatoci daban-daban sun samu damar amfani da hukumomin bincike domin gudanar da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

Jami'an TCN a wajen aiki
Yadda ma'aikatan TCN ke aiki a Najeriya. Hoto: TCN
Source: Twitter

Atiku ya ce majalisar tarayya ta taba gudanar da bincike kan ayyukan wutar lantarki, amma ba a taba gayyatarsa domin ya amsa wata tuhuma ta aikata ba daidai ba.

Atiku zai bude iyakokin Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya yi alkawarin sake bude iyakokin Najeriya domin farfado da kasuwancin da ake yi tsakanin Najeriya da kasashen makwabta idan aka zabe a 2027.

Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC ya ce rufe wasu hanyoyin kan iyaka ya yi matukar illa ga 'yan kasuwa, musamman matasa da suka dogara da kasuwancin ketare.

Atiku ya kuma yi alkawarin bunkasa tashoshin jiragen ruwa na Kudu domin saukaka jigilar kaya zuwa yankuna daban-daban na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng