APC Ta Dauko Salon Wulakanci ga Wike, Ta Nuna Rashin Hada Kai da Shi
- Jam’iyyar APC reshen Jihar Bayelsa ta yi watsi da muhimmancin kawancen siyasa na “Rainbow Coalition” da ke samun karbuwa a jihar
- Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Warman Weri Ogoriba, ya ce jam’iyyar na da tsare-tsare da goyon bayan jama’a a matakin tushe
- Wannan martani ya biyo bayan ikirarin Ministan Abuja, Nyesom Wike, cewa yana da goyon baya da tsarin siyasa da zai taimaka masa a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Bayelsa – Jam’iyyar APC a Jihar Bayelsa ta ce ba za ta damu da kawancen siyasa da ke wajen tsarin jam’iyyar ba, tana mai cewa tana da cikakken tsari da goyon bayan jama’a a jihar.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Warman Weri Ogoriba, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce APC ta kasance dunkulalliya kuma tana da tushe a dukkan kananan hukumomi takwas da mazabu na siyasa na jihar.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa martanin APC ya biyo bayan kalaman Nyesom Wike, wanda ya ce yana da tsarin siyasa da goyon bayan da zai taimaka wajen samun kuri’un Rivers da Bayelsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
APC ta sace wa gwiwar Wike
Ogoriba ya ce APC ba za ta bari kawancen siyasa na daban ya dauke mata hankali ba, yana mai cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kara yawan mambobinta da karfafa hadin kan cikin gida.
Ya kuma ce jam’iyyar za ta kara zurfafa tuntubar jama’a da hada kan magoya bayanta a matakin kasa, musamman yayin da zaben 2027 ke kara matsowa.
Ya ce:
“Abin da ke gaban jam’iyyar shi ne ta kasance cikin tsari, da’a da jajircewa wajen cimma burin ci gaban APC da kuma tallafa wa ’yan takararta a dukkan matakai.
“Muna da yakinin cewa hadewar tsarin jam’iyyar da ke akwai, mambobi masu kishin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da kuma hanyoyin da muke da su a matakin tushe za su samar da ginshikin gudanar da kamfe mai karfi a 2027.”

Source: Facebook
APC ta bukaci hada kai
Shugaban APC na Bayelsa ya bukaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar a fadin jihar su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai tare da mai da hankali kan manufofin jam’iyyar.
Leadership ta wallafa Ogoriba ya tabbatar musu da cewa shugabancin jam’iyyar a jihar zai ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma hada goyon baya a tsakanin al’ummomin jihar.
Ya kuma jaddada cewa shugabancin APC na Bayelsa ya kuduri aniyar karfafa tsarin jam’iyyar da kuma yin aiki tare domin samun nasarar Shugaba Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaben 2027.
Tinubu zai shiga lamarin Wike
A wani labarin, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu na fuskantar kiraye-kirayen shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin wasu gwamnonin APC da Ministan Abuja, Nyesom Wike, yayin da zaben 2027 ke kara matsowa.
Wike ya kasance yana tallata Rainbow Coalition a Rivers da sauran wurare domin neman goyon bayan Tinubu, yayin da wasu shugabannin APC suka nuna damuwa kan tasirin kawancen ga ’yan takarar jam’iyyar.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta ce ana sa ran Tinubu zai tattauna da bangarorin da abin ya shafa domin kokarin sasanta bambance-bambancen da ke tsakaninsu.
Asali: Legit.ng
