Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Kasuwa Dauke da Makamai, Sun Bude Wa Mutane Wuta

Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Kasuwa Dauke da Makamai, Sun Bude Wa Mutane Wuta

  • ‘Yan bindiga sun kai hari wata kasuwar amfanin gona da ke Mangu, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama
  • Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8.30 na daren ranar Juma’a yayin da ‘yan kasuwa ke shirin rufe kasuwar
  • Shugaban kungiyar MDA, Bulus Dabit, ya ce wadanda suka jikkata an kai su asibiton JUTH domin samun kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Yan bindiga sun kai hari wata kasuwar amfanin gona da ke garin Mangu, karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau, a daren Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama a cikin kasuwar ta hatsi.

Plateau.
Taswirar jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

TABLE OF CONTENTS

Yan bindiga sun kai hari kasuwa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna garin Mangu sun ce harin ya faru da misalin karfe 8.30 na dare, lokacin da ‘yan kasuwa da masu sayayya ke shirin rufe kasuwar.

Kara karanta wannan

Matsayar addinin Musulunci kan sayen hannun jarin matatar Dangote

Sun ce lamarin ya jefa ‘yan kasuwa da masu wucewa cikin firgici, lamarin da ya tilasta musu tserewa ta bangarori daban-daban.

Shugaban kungiyar ci gaba Mwaghavul (MDA), Bulus Dabit, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun gudu nan take bayan harin.

Ya kara da cewa wadanda abin ya rutsa da su sun hada da mata da maza a kasuwar, lamarin da ya kara tada hankalin jama'a.

Dabit ya ce har yanzu ba a gano sunayen wadanda aka kashe ba, yayin da aka tura wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) domin yi musu magani.

Yadda maharan suka kashe mutane

“Da misalin karfe 8:00 na daren Juma’a, ‘yan bindiga sun bude wa wata mota da ke barin kasuwar kayan lambu wuta a Mangu, inda suka kashe mata biyu da wani matashi.

“Har yanzu ba a san sunayen wadanda lamarin ya rutsa da su ba. An kuma jikkata wasu masu wucewa ta wurin, sannan aka tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos domin neman magani,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun mamaye gidan kwamishina, sun bude wuta ba tare da nuna tausayi ba

Shugaban MDA ya nuna mamakinsa kan yadda harin ya faru duk da tura daruruwan sojoji yankin kwanan nan, bayan hare-haren da aka kai a wasu sassan karamar hukumar Mangu a watan da ya gabata, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Gwamnan Plateau.
Gwamnan jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya, Barista Caleb Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su yi amfani da fasaha da sauran hanyoyin tattara bayanan sirri wajen gano wuraren da ake zargin maharan suke, tare da kama su kafin su sake kai wasu hare-hare.

Leadership ta ruwaiho cewa garin Mangu ya kasance kusan babu kowa bayan harin, yayin da aka ga jami’an tsaro suna sintiri a yankin domin dawo da doka da oda.

Yan bindiga sun kashe matafiya 9

Kun ji cewa ‘yan bindiga sun kashe aƙalla fasinjoji tara bayan sun buɗe wa motar haya wuta a daidai titin Dungus Junction da ke Jos ta Kudu a Filato.

Mazauna yankin sun shaida wa ‘yan jarida cewa lamarin ya faru ne lokacin da direban motar ya tsaya domin sauke wasu fasinjoji a mahadar, kwatsam sai ga yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262