Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Yi Babban Rashi, Hajiya Nana Asma'u Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu ya jajanta wa Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III kan rasuwar gwaggonsa, Hajiya Nana Asma’u
- Rahotanni sun nuna cewa Nana Asma’u ta rasu ne ranar Talata da ta gabata tana da shekara 100 a duniya
- Gwamna Aliyu ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan gidan sarauta, Jihar Sokoto da Najeriya baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya jajanta wa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, kan rasuwar matar mahaifinsa, Hajiya Nana Asma’u, wadda ta rasu ranar Talata tana da shekara 100.
Gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Musulmi a fadarsa da ke Sokoto, inda ya bayyana rasuwar marigayiyar a matsayin babban rashi ga gidan sarauta, Jihar Sokoto da ƙasar nan.

Kara karanta wannan
Gwamna a Najeriya ya kamu da rashin lafiya har ya gaza fitowa aiki? Gaskiya ta bayyana

Source: Twitter
Gwamna Aliyu ya ce an yi babban rashi
A rahoton Daily Trust, Ahmed Aliyu ya ce Nana Asma’u ta taka muhimmiyar rawa ta uwa a cikin gidan sarauta, yana mai cewa rasuwarta ta haifar da giɓin da zai yi wuya a cike.
“Rasuwar Nana Asma’u haƙiƙa wani babban rashi ne,” in ji gwamnan.
Ya roƙi Sarkin Musulmi da sauran ’yan uwa su karɓi rasuwar a matsayin ƙaddarar Allah Maɗaukaki, tare da addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar kura-kuranta, Ya shigar da ita Aljanna.
Sarkin Musulmi ya gode wa gwamna
A nasa martanin, Sarkin Musulmi ya gode wa Gwamna Aliyu bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kai masa, tare da yi masa addu’ar Allah Ya saka masa da alheri mai yawa.
“Muna addu’ar Allah Ya ba ka tsawon rai domin ka ci gaba da yi wa al'umma hidima,” in ji Sarkin Musulmi.
Gwamnan ya samu rakiyar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko; shugaban APC na jihar, Haruna Adiya; ’yan majalisun dokoki; kwamishinoni; hadimai da sauran abokan siyasar sa.
Malam Bashiru Gidan Kanawa ya jagoranci addu’o’i na musamman domin Allah Ya jiƙan Nana Asma’u da sauran waɗanda suka riga mu gidan gaskiya.
Gwamna ya ziyarci gidaje don ta'aziyya
Gwamnan ya kuma ziyarci wasu iyalan da suka yi rashin ’yan uwansu a cikin birnin Sokoto, ciki har da iyalan Abdullahi Kafinta na Rungumi, wanda ya rasu yana da shekara 80.

Source: Twitter
Sauran iyalan da gwamnan ya ziyarta sun haɗa da na Aisha Umar, mai shekara 87; Abubakar Abdulraheem; Alhaji Garba Shugaba, mai shekara 85; Ahmad Mode na Gagi; da marigayi Aliyu Musa Mana na Mana.
An yi addu’a a dukkan gidajen da gwamnan ya ziyarta domin Allah Ya jiƙan mamatan.
Sarkin Musulmi ya yi ta'aziyyar Sarkin Gumel
Kun ji cewa Sarkin Musulmi ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar Mai martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON.
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce raasuwar basaraken babban rashi ne ga masarautar Gumel, Jigawa da daukacin al'ummar Musulmi.
Asali: Legit.ng
