Zaben 2027: Sabon Umarnin da Tinubu Ya Bayar Ya Jawo an Zarge Shi da Shirin Sayen Kuri'a
- APM ta nuna damuwa kan umarnin Bola Tinubu na sakin kuɗaɗe ga Hukumomin kula da Ci gaban Yankuna gabanin babban zaɓen 2027
- Jam’iyyar ta ce ba ta adawa da sakin kuɗaɗen, amma ta nemi a tabbatar da gaskiya, bin diddigi da cikakken hisabi kan yadda za a kashe su
- APM ta buƙaci gwamnati ta bayyana rabon kuɗaɗen, ayyukan da za a gudanar, wurarensu, kuɗin kowanne aiki da sunayen ’yan kwangila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta nuna damuwa kan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sakin kuɗaɗe ga Hukumomin Kula da Ci gaban Yankuna.
Jam'iyyar APM ta yi zargin cewa matakin na iya samar da damar yin amfani da dukiyar jama’a ba bisa ka’ida ba gabanin zaɓen 2027.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar na ƙasa, Yusuf Abubakar, ya sanya wa hannu, APM ta ce ba ta adawa da sakin kuɗaɗen, cewar rahoton jaridar Leadership.
Sai dai jam’iyyar ta jaddada cewa ya kamata a haɗa sakin kuɗaɗen da matakan tabbatar da gaskiya, riƙon amana da cikakken bayani kan yadda za a yi amfani da su.
APM ta nemi cikakken sa ido
APM ta ce ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin tantance ingancin ayyukan da za a gudanar da kuma irin tasirin da ake sa ran za su haifar.
Ta kuma nemi a riƙa bibiyar yadda ake sakin kuɗaɗen tare da samun sa ido mai zaman kansa kan yadda ake aiwatar da ayyukan.
“Ba mu da wata matsala da sakin kuɗaɗe ga Hukumomin Kula da Ci gaban Yankuna, amma dole ne a haɗa wannan kuɗaɗe da gaskiya, sakamakon da za a iya auna shi, sa ido mai zaman kansa da kuma cikakken riƙon amana,” in ji jam’iyyar.
Jam’iyyar ta nuna shakku kan umarnin
APM ta ce lokacin da aka bayar da umarnin ya ƙara haifar da damuwa kan yadda za a yi amfani da kuɗaɗen, musamman ganin cewa babban zaɓen 2027 na ƙara gabatowa.
Jam’iyyar ta kuma tambayi dalilin da ya sa aka bayar da umarnin watanni bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 1.3 ga Hukumomin Kula da Ci gaban Yankunan a watan Maris.
“Shin ba abin tambaya ba ne cewa umarnin Shugaba Tinubu ya zo ne ’yan watanni kafin zaɓe, watanni shida bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kasafin Naira tiriliyan 1.3 ga Hukumomin Kula da Ci gaban Yankunan a watan Maris?” in ji sanarwar.
APM ya yi zarge-zarge
Jam’iyyar ta kuma yi iƙirarin cewa tarihin gwamnatin APC wajen aiwatar da kasafin kuɗi, tare da zarge-zargen karkatar da kuɗaɗen gwamnati da wasu ’yan jam’iyyar ke fuskanta, ya ƙara sanya jama’a cikin damuwa.
APM ta buƙaci Tinubu ya yi bayani kan damuwar jama’a cewa sakin kuɗaɗen na iya zama hanyar samar da kuɗin da za a yi amfani da shi wajen jan hankalin masu zaɓe gabanin 2027.
“Dole Shugaba Tinubu ya yi wa jama’a bayani kan damuwar cewa umarninsa na iya bai wa APC damar adana kuɗaɗe domin shirinta na ba masu zaɓe kuɗi,” in ji APM.
Sai dai waɗannan zarge-zarge na APM ne, ba tare da wata hujja da aka gabatar a cikin sanarwar da ta tabbatar da su ba.

Source: Twitter
APM ta caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APM ta caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kalaman da ya yi wa limaman cocin Katolika dangane da tattalin arziki da tsaro a Najeriya.
Jam'iyyar ta ce ikirarin shugaban cewa tattalin arzikin kasar ya farfado kuma gwamnatinsa ta ceci Najeriya daga matsalar rashin tabbas bai dace da abin da miliyoyin 'yan Najeriya ke fuskanta ba.
Asali: Legit.ng


