Atiku Ya Dauko Tarihin Abin da Ya Faru da Tinubu a 1993, Ya Aika Sako Fadar Shugaban Kasa
- Atiku Abubakar ya bukaci fadar shugaban kasa ta yi bayani kan kwace $460,000 da gwamnatin Amurka ta yi daga asusun Bola Tinubu a 1993
- Dan takarar ADC ya ce bai kamata fadar shugaban kasa ta mayar da hankali kan bata sunan kamfanin Von Batten-Montague-York ba
- Atiku ya kalubalanci gwamnatin Tinubu kan zargin kashe dala miliyan 9 wajen daukar kamfanin haya a Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci fadar shugaban kasa ta yi bayani kan batun $460,000 da Bola Ahmed Tinubu ya rasa a Amurka a shekarar 1993.
Atiku ya ce maimaikon fadar shugaban kasa ta mayar da hankali wajen sukar Von Batten-Montague-York, L.C., wani kamfani da ke Washington, ya kamata ta amsa tambayoyin da suka shafi batun kudin.

Source: Facebook
The Cable ta rawaito cewa bayanai sun nuna Tinubu ya mika $460,000 ga gwamnatin Amurka a 1993 bayan wata kotu a Chicago ta yanke cewa kudin sun samo asali ne daga harkar safarar hodar iblis.
Dalilin Atiku na daukar kamfanin haya
A watan Maris, Atiku ya dauki hayar kamfanin Von Batten-Montague-York domin karewa da kuma inganta abin da aka bayyana a matsayin martabarsa a Amurka.
Bisa wata takarda da aka shigar a Ma'aikatar Shari'a ta Amurka (DOJ), daya daga cikin manufofin yarjejeniyar shi ne bai wa kamfanin damar daidaita bayanai da gwamnatin Najeriya ke yadawa a Amurka.
Fadar shugaban kasa ta soki Atiku
A ranar Laraba, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Sunday Dare, ya soki Atiku kan daukar kamfanin domin yi masa aiki.
Dare ya ce ya kamata a yi taka-tsantsan da ikirarin cewa Von Batten, babban abokin huldar kamfanin, yana da dama kai tsaye ga Trump ko gwamnatinsa, ko kuma zai iya yin tasiri kan shari'ar da ke gudana a kotunan Amurka.
Atiku ya bukaci bayani kan $460,000
A wata sanarwa da babban mataimakinsa kan hulda da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Laraba, Atiku ya ce fadar shugaban kasa tana mayar da hankali kan tarihin Von Batten maimakon amsa tambayar da ta shafi $460,000.
Ya ce an yi rijistar yarjejeniyar da ya kulla ta dala miliyan 1.2 da kamfanin bisa radin kai a Ma'aikatar Shari'a ta Amurka karkashin dokar Foreign Agents Registration Act (FARA).
Atiku ya ce Tinubu ya kamata ya yi bayani kan zargin alakarsa da wani binciken gwamnatin tarayyar Amurka kan safarar miyagun kwayoyi da wanke kudade.
Ya kuma ce shugaban kasar ya bayyana dalilin kwace $460,000 daga wani asusun da ke dauke da sunansa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Twitter
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na ADC ya zargi fadar shugaban kasa da munafunci kan sukar kudin da ya kashe wajen daukar kamfanin aiki
Ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu ta kulla yarjejeniya da kamfanin DCI Group kan $750,000 a kowane wata.

Kara karanta wannan
Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba
A cewarsa, yarjejeniyar ta kai dala miliyan 4.5 cikin watanni shida, tare da wasu sharudda da za su iya kara kudin zuwa dala miliyan 9.
FBI ta taba kai samame gidan Atiku
Kun ji cewa an tono yadda jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) suka kai samame gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, a Maryland.
Binciken ya shafi William Jefferson, ɗan majalisar Amurka daga New Orleans, da zargin biyan ko shirya biyan kudi ga jami’an Najeriya da Ghana
Asali: Legit.ng

