ICC Ta Saki Yadda Minista Ya Nemi Yaudarar Buhari a Ci $200m a Aikin Mambila
- Abubakar Malami ya yi kokarin sa Muhammadu Buhari amincewa da wata yarjejeniyar da za ta jawo a ci karin $200m
- Kotun ICC ta bayyana cewa ya hada-kai da Leno Adesanya yana neman rashawa lokacin da ake shari'ar aikin Mamabilla
- Tsohon Ministan Shari'a ya so ya yi amfani da shari’ar kasar da kamfanin Sunrise ya samu kudi amma bai yi nasara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - ICC ta bayyana yadda Abubakar Malami SAN ya yi kokarin yaudarar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a ofis.
An zargi Abubakar Malami a lokacin yana ministan shari’a da kokarin aikata ba daidai ba dangane da shari’ar aikin wutan Mamabilla.

Source: Getty Images
Alakar Abubakar Malami da kamfanin Sunrise
Premium Times ta ruwaito cewa ya hada kai da Leno Adesanya na kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Ltd.
Tsohon ministan ya nemi shiga wasu miyagun yarjejeniyoyi da wannan kamfani da yake shari’a da gwamnatin Najeriya a kotu.
A karshe kotun ICC a ranar Alhamis ta yi watsi da ikirarin da kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Ltd yake yi.
Kamfanin ya bukaci $4680m domin a sasanta da shi ban da wasu $2.7bn da yake nema da sunan hakkoki da kuma ruwa da ya taru.
Adesanya ya zargi Malami da neman cin hanci
ICC ya karbi maganganun Leno Adesanya, wanda ya ce Abubakar Malami ya bukaci cin hancin kudi lokacin da ake cikin tattaunawa.
Adesanya ya ce an yi haka ne bayan an sa hannu a yarjejeniyar biyan $200m. Sun yi tattaunawa ta kafar WhatsApp a lokacin.
The Cable ta rahoto kotun yana bayanin yadda aka shiga wata yarjejeniya ta rashin gaskiya tsakanin ministan shari’ar da kamfanin.
Wannan ya kawo matsala a wata yarjejeniya da aka cin ma a baya, kuma a karshe aka bar Najeriya da yiwuwar kashin $400m.
Ministocin Buhari sun nemi $200m ta dawo $400m
A farkon 2020 an sa hannu Najeriya za ta biya $200m domin a sasanta da kamfanin, a Maris kwatsam aka ji karin wasu $200m.
Rahoton ya ce alamomin tambayan da aka sun shafi Malami da takwaransa a majalisar FEC, Minista makamashi wato Saleh Mamman.
Adesanya ya fada wa kotu cewa Malami da Mamman sun ce za a biya $200m a farat daya, ragowar kuma sai ‘ya yi abin da ya dace.’
Wanda ya bada shaidan a kotu ya yi ikirarin yana da hujjojin maganar a sauti da bidiyo, amma ba a kai ga karbar hujjojin nasa ba.
Muhammadu Buhari bai fada tarkon Malami ba
An ce Malami ya gagara gamsar da Muhammadu Buhari ya sa hannu a sabuwar yarjejeniyar domin a biya karin kudin nan.
A Junairun 2021, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya aika wa Malami takarda, ya sanar masa da kin amincewarsa.
Duk da haka ya yi ta kokarin ya shawo kan shugaban kasar, amma bai yi nasara ba.

Source: Getty Images
Sunrise: Gwamnatin Najeriya ta yi nasara a kotu
Rahoto ya gabata a baya dangane da nasarar da gwamnatin Najeriya ta samu a kan Sunrise Power and Transmission Company Ltd.
Ana ta rikici a kotu ne tun 2003 game da aikin wutar Mambilla a Taraba wanda zai bada damar samun megawatt 3960 na lantarki.
Hukuncin kotun ya bukaci kamfanin ya maida wa Najeriya $11.8m na kudin shari’a, ya kuma yi fatali da bukatar biyan wasu miliyoyi.
Asali: Legit.ng


