Tinubu Ya Saka Lokacin Samun Saukin Sufuri bayan Zama da Gwamnoni

Tinubu Ya Saka Lokacin Samun Saukin Sufuri bayan Zama da Gwamnoni

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a kafa karin tashoshin shan man gas na CNG guda 500 a fadin Najeriya
  • Hakan zai kara yawan tashoshin CNG da ake shirin kafawa karkashin Shirin Shugaban Ƙasa na CNG zuwa guda 1,000
  • Tinubu ya ce daga ranar 1 ga Oktoban 2026 gwamnati na fatan 'yan Najeriya su fara cin moriyar rage farashin CNG

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya umarci a kara kafa tashoshin man CNG guda 500 a fadin Najeriya domin taimakawa wajen rage kudin sufuri.

Tinubu ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da kungiyar gwamnonin Najeriya a ranar Alhamis, inda ya ce gwamnonin sun kuduri aniyar daukar matakan rage kudin sufuri a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Ribadu, Dikko Radda da mutum 10 da Tinubu ya manta da su a kwamitin yakin zabe

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, shugaban ya ce gwamnatinsa na zuba jari mai yawa wajen sauya tsarin makamashi, musamman ta hanyar fadada cibiyoyin sauya motoci zuwa amfani da CNG.

Za a kafa tashoshin CNG 500

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Alhamis, Tinubu ya ce karin tashoshin 500 zai hade da tashoshin 500 da aka bayar da umarnin kafawa a farkon shekarar.

Ya ce hakan zai sa adadin tashoshin CNG da ake shirin samu a karkashin shirin ya kai 1,000 a fadin kasar.

Tinubu ya ce sama da motoci 120,000 ne aka riga aka sauya su zuwa amfani da CNG a Najeriya, yayin da ake shirin samar da karin na'urorin sauya motoci sama da 100,000.

Ya ce gwamnati na kuma ci gaba da fadada cibiyoyin sauya motocin da tashoshin man CNG a sassa daban-daban na kasar.

Punch ta rahoto cewa shugaban ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na daukar nauyin ayyukan gas sama da 100 a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

Batun rage kudin sufuri

Shugaban ya ce fadada tashoshin CNG na da muhimmanci musamman wajen rage kudin sufuri a cikin jihohi, inda ya ce al'umma ke jin radadin tsadar sufuri kai tsaye.

Tinubu ya bayyana cewa motar da ke amfani da CNG na kashe kashi 60 zuwa 80 cikin 100 wajen sayen man fetur idan aka kwatanta da wadda ke amfani da fetur.

Wasu motocin lantarki da aka raba
Motocin lantarki da gwamnatin Najeriyata kaddamar a Abuja. Hoto: @OwanEnoh
Source: Twitter

Ya ce gwamnati na son ganin 'yan Najeriya sun fara cin gajiyar wannan ragin daga ranar 1 ga Oktoba ta hanyar saukar da kudin sufuri.

Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi sun amince da kafa kwamitin hadin gwiwa da zai fara aiwatar da matakan rage kudin sufuri nan take.

An kaddamar da motocin bas 100

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da motocin bas 100 masu amfani da wutar lantarki a Abuja .

An kaddamar da motocin ne a ranar Laraba a Eagle Square da ke Abuja domin rage matsalolin sufuri da inganta jin dadin ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Rahoto ya nuna cewa matakin farko na shirin ya kunshi motocin bas 37 daga cikin 100 da aka amince da samarwa karkashin shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng