Atiku zai Bude Iyakokin Najeriya da aka Rufe Tun Lokacin Buhari
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai sake bude iyakokin Najeriya da kasashen makwabta idan aka zabe shi
- Atiku ya ce rufe iyakokin kasa ya jefa matasa da dama cikin rashin aikin yi tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci tsakanin kasashe
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce zai bunkasa tashoshin ruwan Kudu domin saukaka jigilar kaya zuwa Arewa maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai sake bude iyakokin Najeriya da kasashen makwabta idan aka zabe shi.
Atiku ya ce rufe iyakokin kasa ya kawo babban cikas ga kasuwancin da ake yi tsakanin Najeriya da kasashen makwabta tare da jefa matasa da dama cikin rashin aikin yi.

Kara karanta wannan
'Ban da Atiku,' Dan takara 1 da ya bugu kirji kan shi kadai zai iya maido tallafin mai

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a wani bidiyo.
Atiku zai bude iyakokin Najeriya
Atiku ya ce jihohin Arewacin Najeriya suna da iyaka da kasashe irin su Kamaru, Chadi, Nijar da Jamhuriyar Benin.
Ya ce matasa da dama sun dogara da harkokin safarar kayayyaki da kasuwanci tsakanin Najeriya da wadannan kasashe domin samun abin dogaro.
A cewarsa:
"Jihohin Arewa suna da iyaka da Kamaru, Chadi, Nijar da Jamhuriyar Benin, amma sai ka rufe dukkan wadannan iyakoki."
Ya ce:
"Duk matasanmu da suke kasuwanci tsakanin wadannan kasashe, suna jigilar kayayyaki daga wannan kasa zuwa waccan. Wannan kasuwanci ne na halal tsakanin kasashe."
Gwamnatin tarayya ta rufe wasu iyakokin kasa a watan Agustan 2019 a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari duk da an bude wasu daga baya.
'Matasa sun rasa jari'
Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce rufe iyakokin ya jefa wasu matasa cikin matsalar tattalin arziki, inda wasu suka rasa jarin da suka tara tsawon lokaci.
A cewarsa, wasu daga cikin matasan suna da jarin da ya kai Naira miliyan 10 ko Naira miliyan 20, tare da daukar wasu mutane aiki a karkashin sana'o'insu.

Source: Facebook
PM News ta wallafa cewa ya ce rufe iyakokin ya sa wasu daga cikinsu suka durkushe tare da rasa hanyoyin samun abin dogaro.
Atiku zai bunkasa Kudu
Atiku ya kuma ce ya tattauna da wasu kamfanonin jigilar kaya da na bunkasa harkokin jiragen ruwa a Turai kan yadda za a raya tashoshin ruwa da ke Kudancin Najeriya.
Ya ce bunkasa tashoshin zai samar da daidaito wajen shigo da kaya tare da saukaka safarar su zuwa sauran sassan Najeriya.
A cewarsa, idan aka sauke kwantena a tashoshin Calabar, Uyo ko Port Harcourt, zai kasance da sauki a kai su zuwa Yola da sauran yankunan Arewa maso Gabas.
Atiku ya ce a halin yanzu yana iya daukar sama da watanni biyu kafin a kai kwantena daga Legas zuwa Yola saboda nisa da kuma matsalolin hanyoyi.
Batun maido tallafin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce jam'iyyarsa za ta dawo da tallafin man fetur idan ta samu nasarar lashe zabe.
Sowore ya ce AAC ce kadai ta bayyana matsayinta karara cewa ba za ta cire tallafin man fetur ba, yana mai zargin wasu 'yan siyasa da sauya matsayinsu saboda maslahar siyasa.
Ya kuma caccaki Atiku Abubakar da wasu 'yan siyasa, yana mai cewa bai kamata su yi ikirarin cewa su ne suka fara daukar matsaya kan batun tallafin man fetur ba.
Asali: Legit.ng

