2027: Atiku Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro a cikin Shekara 1

2027: Atiku Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro a cikin Shekara 1

  • Atiku Abubakar zai dauki sababbin jami'an tsaro, ya ba su kayan aiki idan aka zabe shi a takarar karshe ta 2027
  • Ya ce zai taimaki matasa da jarin sana'o'i don raba su da zaman banza duk saboda a samu tsaro a shekarar farko
  • Atiku zai gyara alaka da makwabta kuma ya hada kai da shugabannin ECOWAS don farfado da dakarun ECOMOG

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin ADC ya sha alwashin magance matsalar tsaro.

Idan har ‘yan Najeriya suka mara masa baya ya karbi shugabanci, ya ce a shekara daya zai kawo zaman lafiya a kasa.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar mai neman mulki a ADC a gidansa Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya kuma daukar alkawari

Atiku Abubakar ya dauki wannan alkawari ne a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi jim kadan bayan kada gangar siyasa.

Kara karanta wannan

Kofa ya ce APC za ta lashe Kano baki daya, Kwankwaso zai rasa kujeru a 2027

Wazirin Adamawa ya bayyana cewa zai dauki wasu dabaru da za su kawo karshen matsalar da aka dade ana fama da ita.

Rashin tsaro zai zama tarihi ne a shekarar farko da gwamnatin Atiku za ta yi a ofis.

‘Dan takaran jam’iyyar hamayyar ya ce ba zai dauki fiye da shekara guda a fadar Aso Rock Villa bai magance matsalar ba.

Ta ya Atiku zai magance rashin tsaro?

Daga cikin hanyoyin da Atiku zai bi akwai daukar karin jami’an tsaro tare da ba su isassun kayan yakin da za su bukata.

Bugu da kari, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta taimaka wa matasa da jari domin su yi sana’o’i dabam-dabam.

Idan matasa suna zaman banza ne yake ganin ana amfani da su wajen kawo tashin hankali.

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya yana mai sa ran cewa idan gwamnatinsa ta yi wannan, za a nemi rashin tsaro a rasa.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

Gwamnatin Atiku za ta gyara alaka a ECOWAS

Daily Trust ta rahoto shi yana cewa zai hada kai da kasashen ECOWAS na yammacin Afrika domin farfado da dakarun ECOMOG.

Sojojin da ke karkashin rundunar suna da rawar da za su taka wajen yaki da rashin tsaro a sauran kasashen da ke cikin Afrika.

Gwamnatin Atiku za ta nemi hadin-kan har Côte d’Ivoire, Sierra Leone da kasar Liberia saboda nahiyar ta zauna lafiya.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar da hoton wata hanya inda ake fama da matsalar tsaro a Warri Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Najeriya da Nijar daya ne in ji Atiku

Ya tuno da tsohuwar alakar da ke tskanin Najeriya da Nijar, yake cewa bai kamata juyin mulkin da aka ayi ya bata zumunci.

An ji shi a hirar yana cewa bai ga dalilin da zai sa Najeriya ta yanke hulda da Nijar ba saboda kurum sojoji sun kifar da gwamnati.

Baya ga Nijar, ya ce zai dawo da Burkina Faso da Mali cikin ECOWAS domin rage adadin masu zaman kashe wando a kasashen.

'Yan bindiga sun dauke masu bautar kasa

Kara karanta wannan

EFCC ta yi tayin lada ga masu kwarmato game da dukiyoyin Najeriya da aka wawure

Dazu ake jin 'yan bindiga sun yi garkuwa da mambobin NYSC 15 a jihar Kogi lokacin da suke komawa gida daga sansanin Bayelsa.

Rukunin masu bautar kasar sun kasance suna tafiya ne a cikin wata motar bas lokacin da tsagerun suka tare su tare da tafiya da su zuwa daji.

Wannan ta'adi da aka yi a kan hanyar Abuja ya kara nuna yadda ake fama da garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng