Tsofaffin Shugabannin Majalisa Sun Tsaida ‘Dan takara, har da Masa Alkawarin Kuri’u Miliyan 11

Tsofaffin Shugabannin Majalisa Sun Tsaida ‘Dan takara, har da Masa Alkawarin Kuri’u Miliyan 11

  • Shugabannin da aka yi a baya a Majalisar dokoki a jihohi sun kira wani babban taro na kasa a birnin Abuja
  • A karshen zaman da aka yi, tsofaffin ‘yan majalisar sun yarda cewa za su goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2027
  • ‘Yan kungiyar FOPSHAN sun gamsu da gwamnatin APC kuma za su bada gudumuwar kuri’u miliyan 11

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsofaffin shugabanni a Majalisar dokokin jihohi a Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga Bola Ahmed Tinubu.

A zaben shugaban kasa da za a yi a 2027, kungiyar FOPSHAN tana tare da tikitin Bola Tinubu da Kashim Shettima a APC.

FOPSHAN
Taron da FOPSHAN ta goyi bayan Bola Tinubu Hoto: von.gov.ng
Source: UGC

FOPSHAN suna tare da Bola Tinubu

Hukumar dillancin labarai na kasa wato NAN ta ce FOPSHAN ta bayyana haka ne a wajen taro na kasa da ta shirya.

Kara karanta wannan

Yadda kawancen tallata Tinubu da Wike ya kafa yake neman tarwatsewa

An yi wannan taro ne a fadar Aso Rock a Abuja a ranar Alhamis da nufin nuna goyon baya ga gwamnatin APC.

Taron ya yaba da jajirtattun manufofin da shugaba Tinubu ya dauka cikin shekaru uu Najeriya.

Tsofaffin shugabannin majalisar sun yarda cewa manufofin da aka kawo sun kawo matsin lambar tattalin arziki in ji VON.

Sai dai duk da haka, sun gamsu cewa cire tallafin man fetur yana dauke da amfanin da jama'a za su mora a nan gaba.

Tsofaffin 'yan majalisa za su ba Tinubu kuri'u

Kungiyar ta sha alwashin nemo wa Tinubu kuri’a miliyan 11 a zaben shekara mai zuwa.

Baya ga haka, sun nuna goyon bayansu ga wasu sauye-sauye da aka kawo da suka canza fasalin shugabanci a yau.

Daga cikinsu akwai kafa hukumomin raya yankuna, ba kananan hukumomi ‘yanci da kafa ‘yan sandan jihohi.

‎Sakataren FOPSHAN na kasa, Matog Dogara ya karanto matsayar da duka ‘yan kungiyar suka dauka a taron.

Kara karanta wannan

Zargin cin kudi ya kai ‘dan takaran APC a zaben majalisa cikin ragar hukumar ICPC

Premium Times ta rahoto cewa kungiyar ta amince da zaben Remi Tinubu a matsayin babbar uwar FOPSHAN.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim ya gabatar da jawabi a matsayin shugaban taron.

Manufofin shugaba Tinubu sun sha yabo

Anyim Pius Anyim yake cewa Tinubu ya wuce ‘dan siyasa, dattijo ne da yake kokarin gyara makomar ‘yan Najeriya.

Sai nan gaba za a ci moriyar matakan da gwamnati ta ke dauka a cewar Anyim wanda ya taba zama sakataren gwamnati.

Simon Lalong ya yi jawabi a wajen a matsayinsa na sanata kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki.

Tsohon gwamnan ya kare janye tallafin mai da sauyin da aka kawo a canjin kudi, bashi, haraji da neman kudin shiga.

Kafin shugaban kungiyar, Wasiu Eshilokun ya yi jawabinsa, Ministan mai, Heineken Lokpobiri shi ma ya ce wani abin.

Bola Tinubu
Bola Tinubu lokacin kamfe da hoton shi bayan shiga ofis Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Yan darika za su zabi Tinubu da Radda

Rahoto ya ce kungiyoyin ɗariƙa a Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umaru Radda.

Kara karanta wannan

Yakin zaben 2031 da abubuwan da suka haddasa rigimar Wike da gwamnonin APC

A wani taro na raba tallafi a Katsina, jagororin dariƙa karkashin ma'assasar Sheikh Ɗahiru Bauchi sun bayyana goyon bayansu ga 'yan APC.

Sun ce gwamnatin jihar ta yi koyi da tsohon gwamna Aminu Bello Masari wajen damawa da mabiya ɗariƙa, saboda haka za su yi ta a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng