Tinubu Ya Yi wa Gwamnoni Umarni domin Inganta Rayuwar Talaka

Tinubu Ya Yi wa Gwamnoni Umarni domin Inganta Rayuwar Talaka

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana sane da irin wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauyensa
  • Gwamnan ya ce duk da cewa wasu muhimman alamomin tattalin arzikin Najeriya suna samun sauki, tasirin hakan bai kai ga talakawa da sauran 'yan kasa ba tukuna
  • Sule ya ce Tinubu ya umurci gwamnonin jihohi da su kara mayar da hankali kan ayyukan karkara, samar da ruwa, wutar lantarki da shirye-shiryen tallafa wa jama'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lafia – Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana sane da irin wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

Sule ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar Nasarawa da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Lafia.

Kara karanta wannan

Asiri ya kara tonuwa: Majalisa ta gano hukumomin bogi 12 da kafa a mulkin Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya san halin da ake ciki

Punch ta wallafa cewa gwamnan ya ce shugaban kasa ya fahimci cewa duk da yadda wasu muhimman alamomin tattalin arziki ke samun sauki, har yanzu talakawa ba su fara jin tasirin wannan saukin yadda ya kamata ba.

"Shugaban kasa ya ce wadannan su ne kalubalen, wadannan su ne matsalolin,"

In ji Gwamna Sule yayin da yake yi wa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar bayani.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce Tinubu ya umurci gwamnonin da su ci gaba da gudanar da manyan ayyukan raya karkara domin inganta rayuwar jama'ar kauyuka.

Ayyukan da Tinubu ya ce a yi

Sule ya ce shugaban kasar ya bukaci gwamnonin da su ci gaba da gina hanyoyi a karkara, samar da ruwa da wutar lantarki, tare da aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa jama'a.

"Ku ci gaba da gina manyan hanyoyin karkara domin hakan zai taimaka wa mutanen kauyuka. Ku samar wa wadannan mutane ruwa. Ku samar musu da wutar lantarki. Ku kuma shiga cikin wasu shirye-shiryen karfafa tattalin arzikinsu,"

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya fito ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa yake neman mulkin Najeriya a 2027

In ji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa asusun ajiyar kudin wajen Najeriya ya karu daga kasa da dala biliyan 30 zuwa sama da dala biliyan 50, har yanzu hakan bai yi tasiri a rayuwar talaka ba yadda ya kamata.

Gwamna Abdullahi Sule
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule. Hoto: Gov Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Ya ce mutum daga Angwan Takpa idan aka gaya masa cewa asusun ajiyar kudin waje ya haura dala biliyan 50, zai iya tambayar yadda hakan zai taimaka masa.

Tinubu ya yabi Shettima

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, sun taya Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima murnar cika shekaru 60 da haihuwa.

Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin amintaccen aboki, dan kishin kasa kuma ma'aikacin gwamnati mai kishin aiki, tare da yaba masa kan biyayyarsa ga jam'iyyar APC da goyon bayan gwamnatinsa.

Shugaban kasar ya kuma yabawa tarihin Shettima a harkar banki da kuma irin gudunmawar da ya bayar ga jihar Borno da Najeriya, yana mai cewa jajircewarsa wajen ganin an samu ci gaba da hadin kan kasa abin a yaba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng