Trump Ya Gane Wanda ke Samun Nasara a Yakin Amurka da Kasar Musulunci ta Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa na cin nasara a yaƙin da take yi da Iran kuma ya bayyana cewa yaƙin zai ƙare nan ba da jimawa ba
- Donald Trump ya yi wannan magana ne kwana guda bayan ya ce yana nazarin yiwuwar “shafe” Iran gaba daya
- Iran ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya domin warware matsaloli da komawa kan yarjejeniyar da aka cimma a Islamabad
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi magana kan rikicin da kasarsa ke ci gaba da yi da Jamhuriyar musulunci ta Iran yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Fadar White House.
Shugaba Trump ya ce Amurka na cin nasara yaƙin “sosai” kuma yaƙin zai ƙare nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Source: UGC
Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa wannan magana ta zo kwana guda bayan Trump ya ce yana tunanin ko zai “shafe” kasar Iran gaba daya.
“Shin ina son shiga in shafe su, ko kuma ba na so?” Trump ya bada amsa, inda ya shaida wa manema labarai a jiya Juma'a cewa, “Wannan babbar shawara ce. Komai na iya faruwa da ni.”
Iran na son komawa yarjejeniya
A halin da ake ciki, Ali Zeynivand, kakakin Ma’aikatar Cikin Gida ta Iran, ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya da shiga tsakani na ƙasashen duniya domin warware matsalolin da kuma komawa kan yarjejeniyar da aka yi a birnin Islamabad.
“Ana ci gaba da koƙari da shiga tsakani na diflomasiyya daga ƙasashen duniya domin warware matsalolin da komawa kan yarjejeniyar Islamabad da aka cimma,” in ji Zeynivand.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke kusa da gwamnati, Zeynivand ya ce Iran na buƙatar “ɗayan ɓangaren (watau Amurka) ya cika alkawurransa da ke cikin wannan yarjejeniya”.

Kara karanta wannan
Gwamna a Najeriya ya kamu da rashin lafiya har ya gaza fitowa aiki? Gaskiya ta bayyana
Iran ta nemi Amurka ta cika alkawari
Jami’in ya jaddada cewa yarjejeniyar “yarjejeniya ce da Majalisar Tsaron Ƙasa ta Ƙoli ta amince da ita, kuma jagoran ƙoli ya tabbatar da ita, don haka ana ɗaukarta a matsayin hukuncin gwamnati na hukuma”.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da aikin “diflomasiyya mai ƙarfi” tare da halartar shugaban ƙasar Iran a tarukan Shanghai da BRICS da aka gudanar a Indiya da Kyrgyzstan.

Source: Getty Images
Baya ga haka, ya ce gwamnatin Iran na ci gaba da tattaunawa da neman shawarwari don tabbatar da an klma kan wannan yarjejeniya ta Islamabad.
Trump ya yi barazana ga Tarayyar Turai
A wani labarin daban, kun ji cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage cinikayya da Tarayyar Turai ko kuma kakaba mata haraji mai tsanani.
Trump ya yi barazanar ne bayan Tarayyar Turai ta gabatar da shirin bai wa Kanada damar zama mamba 'yar kungiyar a daidai lokacin da Amurka ke takun saka da kasar.
Trump ya bayyana shirin a matsayin abin da yake ganin ba shi da ma’ana, yana mai cewa zai ɗauki matakin da ya dace idan ya ɗauki shirin a matsayin wani hari ga Amurka.
Asali: Legit.ng