Babbar Magana: Atiku Ya Bayyana 'Barayin' da Yake Fafatawa da Su a Zaben 2027
- Atiku Abubakar da ke takarar shugaban kasa a inuwar ADC ya zargi masu mulki da satar zabe da kuma lalata tattalin arzikin Najeriya
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sake tabbatar da cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a 2027
- Atiku ya ce cire tallafin man fetur ya jefa karin ‘yan Najeriya cikin talauci, yayin da Tinubu ya soki manufarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana mutanen da yake fafatawa da su don neman shugabancin Najeriya.
Atiku ya ce yana fafatawa da wasu ‘yan siyasa da ya zarga da satar zabe da kuma lalata tattalin arzikin Najeriya.

Source: Facebook
Atiku, wanda ke cikin fitattun ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2027, ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Talata, 25 ga watan Agustan 2026.
‘Muna fafatawa da barayi’
Yayin da yake jawabi ga wasu daga cikin magoya bayansa, Atiku ya zargi wadanda ke mulkin kasar da yin almundahana.
“Muna fafatawa da barayi. Sun sace zaben. Yanzu sun sace tattalin arzikin kasa. Sun sace komai,” in ji Atiku.
Sai dai kalaman nasa sun zo ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa da fafatawa tsakanin jam’iyyu gabanin babban zaben 2027.
Atiku ya sake alkawarin dawo da tallafin fetur
Atiku ya kuma sake tabbatar da cewa idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027, zai dawo da tsarin tallafin man fetur.
Ya yi wannan karin bayani ne bayan wasu kalamai da aka danganta ga mai magana da yawunsa, Paul Ibe, wadanda suka nuna cewa gwamnatin Atiku za ta iya dawo da tallafin sannan daga baya ta sake cire shi.
Atiku ya ce wasu ‘yan Najeriya sun tuntube shi domin neman karin haske kan matsayinsa game da tallafin.
“Ina so na sake tabbatar da cewa abin da na ce zan dawo da tallafin mai, zan dawo da shi. Najeriya tana da arzikin da zai iya kula da jin dadin ‘yan kasarta,” in ji shi.
Ya soki zare tallafin fetur
Atiku ya bayyana cewa bai amince da cire tallafin man fetur ba, yana mai cewa matakin ya kara jefa ‘yan Najeriya cikin matsanancin talauci.
Ya kuma bayyana cewa Paul Ibe bai yi magana ne a madadinsa ba wajen bayyana wata manufa ta daban game da tallafin.
“Ya kamata a bayyana karara cewa bai yi magana da ikon da nake da shi ba, domin cire tallafin ya jefa karin ‘yan Najeriya cikin talauci fiye da kowane lokaci,” in ji Atiku.
Ya kara da cewa babban nauyin da ke kan gwamnati shi ne kula da jin dadin jama’a da kuma tabbatar da tsaron kasa.
Tinubu ya soki alkawarin Atiku
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taba sukar shawarar Atiku ta dawo da tallafin man fetur, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar rashin fahimta mai tsanani game da shugabanci da tattalin arziki.
Sai dai Atiku ya tsaya kan matsayinsa, yana mai cewa manufarsa ita ce rage radadin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta tun bayan cire tallafin man fetur.
Ya ce idan ya samu damar jagorantar Najeriya, zai mayar da hankali wajen inganta jin dadin jama’a tare da tabbatar da tsaro a fadin kasar.

Source: Facebook
Atiku ya kafa sharadin zuwa muhawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya bayyana sharadin halartar muhawarar ’yan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
Atiku ya tabbatar da cewa zai halarci muhawarar ne kawai idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka halarta.
Asali: Legit.ng


