'Na San Ainihin Shekarun Shugaba Tinubu': Atiku Ya Ce Yana da Hujjoji Masu Ƙarfi
- Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ce yana da hujjar ainihin shekarun Shugaba Bola Tinubu
- Atiku ya ce yana da kwarewa, cancanta da kishin kasa, don haka yake ganin ya cancanci sake neman shugabancin Najeriya a zaben 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya danganta matsalar rashin tsaro da rashin kulawar gwamnati, yana mai cewa za a iya shawo kan rikicin cikin shekara guda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar a zaben 2027 ya yi magana kan shekarun Bola Tinubu.
Atiku ya ce yana da hujjar mai karfi da zai tabbatar Shugaba Bola Tinubu ya kai shekaru 90 a duniya.

Source: Facebook
Atiku ya magantu kan shekarun Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa, inda yake bayanin dalilin da ya sa yake ganin ya cancanci neman shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Atiku ya gano shaidar da ke nuna asalin shekarun Bola Tinubu a duniya
Atiku ya ce:
“Ina da shugaban kasa mai shekaru 90 a yanzu, kuma wanda ba shi da lafiya. Ni ina cikin koshin lafiya; ina da karfi. Don haka me zai hana in ba da kaina domin yi wa ’yan uwana ’yan kasa hidima?, ina da hujjar cewa yana da shekaru 90, kuma zan gabatar da ita a kotu.”
Da yake magana kan tarihin siyasarsa, Atiku ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi damar sake neman shugabancin kasar.
Dan takarar ADC ya ce ya taba neman kujerar gwamna sau hudu, amma hukumomin soji da ke kula da mika mulki ga farar hula sun hana shi takara a lokuta daban-daban.
Ya ce:
“Na tsaya takarar gwamna sau hudu, saboda a lokacin mutanen da ke kula da mika mulkin Najeriya ga dimokuradiyya sojoji ne, kuma ni ina matukar adawa da mulkin soja."

Source: UGC
Kalubalen da Atiku ya fuskanta a rayuwarsa
Atiku ya kara da cewa bai taba samun wani abu cikin sauki a rayuwarsa ba, yana mai cewa hakan ba sabon abu ba ne a tarihin siyasarsa.
"Ban taba samun wani abu cikin sauki a rayuwata ba. Babu wani sabon abu a nan. Don haka, kasancewar ina sake neman shugabancin kasa a karo na biyu ko na uku, ba wani abin mamaki ba ne a rayuwata ta siyasa.”
- Atiku Abubakar
Atiku ya ce yana da kwarewa, cancanta da kishin kasa, don haka yake ganin ya kamata ya yi amfani da wadannan abubuwa wajen yi wa Najeriya hidima.
Da yake magana kan matsalar rashin tsaro a Najeriya, Atiku ya danganta ci gaba da rikicin da “rashin daukar nauyin gwamnati".
Atiku ya fadi dalilin shirin cire tallafi
An ji cewa Atiku Abubakar ya ce bai yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma yana tambayar inda kudaden da aka samu daga cire shi suka tafi.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce kudaden ya kamata a yi amfani da su wajen rage talauci, inganta ilimi da samar da ayyukan yi.
Atiku ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a 2027, domin rage radadin da tattalin arziki ya jefa ‘yan Najeriya ciki.
Asali: Legit.ng
